Buhari Ya Jiƙa Masa Aiki: Hukuma Ta Fadawa Tinubu Bai Isa Ya Ci Wani Bashi ba
- DMO ta fadawa Gwamnatin tarayya ta guji abin da zai jawo a nemo bashi a halin da ake ciki
- Fiye da 70% na abin da ke shigowa cikin aljihun gwamnati ya na komawa ne wajen biyan bashi
- Hukumar kula da bashin ta bada shawarar a san yadda za a iya domin harajin da ake samu ya karu
Abuja – Hukumar DMO mai kula da bashi a Najeriya, ta gargadi gwamnatin tarayya game da karin karbo aron kudi a irin halin da ake ciki a yanzu.
Va5nguard ta ce an fadawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama dole ya gujewa cin bashi.
Hukumar ba ta goyon bayan cin bashi ganin cewa 73.5% na kudin shigan da za a samu a bana duk zai tafi ne a wajen biyan bashin da aka karbo.
Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi
Kamar yadda DMO ta bayyana, kason kudin shigan da su ke tafiya wajen biyan tsofaffin bashi ya yi yawan da bai dace a sake karbo aron kudi ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A fadada hanyar samun kudi
Haka zalika hukumar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta nemi hanyoyin da za tayi wajen ganin ta kara samun kudin shiga a cikin lalitar Najeriya.
Idan ana so gwamnatin Najeriya ta iya cin bashi hankali kwance, rahoton ya ce wajibi ne harajin da za a samu a kasafin kudin shekarar nan ya karu.
An yi hasashen samun kudin shiga na Naira Tiriliyan 10.49, DMO ta ce sai gwamnati ta samu abin da ya kai Naira Tiriliyan 15.5 sannan a iya karo bashi.
Wadannan shawara su na cikin gargadin da aka yi wa sabuwar gwamnati bayan nazarin halin kasar. Punce ta ce bashin Najeriya ya doshi N81tr.
Abin da masana su ka gano
Bincike da MAC ta gudanar a kan bashin Najeriya ya nuna kason arzikin kasa ga bashi ya karu zuwa 37.1% a shekarar 2023 bayan ya na 23.4% a 2022.
Ko da bashin da ke kan wuyan Najeriya ya karu, binciken ya ce an rage wa’adin lokacin biya.
Abin da masana ke yankewa shi ne ka da bashin da ake biya ya wuce 50% na kudin shigarta, lamarin Najeriya ya yi muni da 73% za su tafi ga biyan bashi.
Haka zalika kason jimillar tattalin arziki ga adadin bashi bai dace ya zarce 40%, na Najeriya ya zarce. Wannan ya tilastawa DMO jan hankalin gwamnati.
Za ayi nade-naden mukamai
Ana da labari cewa za ayi rabon mukamai tun da an bada sanarwa Bola Ahmed Tinubu ya sallami daukacin shugabannin hukumomi da ma’aikatu.
A halin yanzu ana shirin nada sababbin shugabannin majalisun da ke kula da hukumomin tarayya. Hakan zai bada damar nada mutum kusan 2000.
Asali: Legit.ng