Tinubu, Shettima Da Sauran Yan Siyasa Sun Samu Karin Albashi Da Kashi 114 Yayin Da NLC Ke Neman A Kara Albashi

Tinubu, Shettima Da Sauran Yan Siyasa Sun Samu Karin Albashi Da Kashi 114 Yayin Da NLC Ke Neman A Kara Albashi

  • Hukumar RMAFC ta amince da karin albashin 'yan siyasa da ma'aikatan shari'a da masu rike da mukamai da kashi 114
  • 'Yan siyasar sun hada da shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnoni da 'yan majalisu da sauran masu mukamai a gwamnati
  • A tsarin mulki, RMAFC ce ke da alhakin duba tare da kawo sauyi a fasalin albashin 'yan siyasa da ma'aikatan shari'a da sauransu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Hukumar Kula da Rarrabe Kudaden Shiga (RMAFC) ta amince da karin fiye da kashi 100 na albashin zababbun 'yan siyasa a kasar.

'Yan siyasar da abin ya shafa sun hada da shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnoni da 'yan majalisun Tarayya.

RMAFC ta kara albashin Tinubu, Shettima da sauran 'yan siyasa albashi da kashi 114
Shugaban kasa, Bola Tinubu Da Mataimakinsa, Kashim Shettima. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Sauran sun hada da ma'aikata a fannin shari'a da sauran masu rike da ofisoshin gwamnati, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tsige Duk Masu Kula da Hukumomi, Cibiyoyi da Kamfanonin Gwamnati

RMAFC ke da hurumin sauya fasalin albashin masu rike da madafun iko

A kundin tsarin mulki, RMAFC ce ke da alhakin duba tare da sauya fasalin albashin masu rike da mukaman siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar ta bukaci 'yan majalisun jihohin kasar da su yi gyaran dokar da ta bada damar sauya fasalin albashin 'yan siyasa da sauran wadanda abin ya shafa.

Shugaban hukumar, Muhammadu Shehu wanda ya samu wakilcin kwamishinar Tarayya, Rakiya Tanko-Ayuba shi ya yi wannan kira a Birnin Kebbi yayin gabatar da sauye-sauyen ga gwamnan jihar, Dakta Nasiru Idris.

Ya ce sauya fasalin albashin ya fara ne tun daga watan Janairu 2023, inda yace ba a sake duba sauya fasalin ba tun 2007, kamar yadda rahotanni suka tattaro.

A cewarsa:

"Iko ne na wannar hukumar ta tabbatar da sauya fasalin albashin 'yan siyasa kamar yadda tsarin doka ya tanada.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba Kabir Ya Ce Ba Za Su Yi Asara Ba, Zai Yi Amfani Da Burbushin Rushe-rushen Don Gyara Ganuwoyin Kano

"Shekaru 16 kenan tun bayan sauya fasalin da akayi, yana da muhimmanci yanzu a sake duba fasalin albashin kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulki."

Ya ce hukumar ta bi doka wurin tsara fasalin albashin

Ya ce hukumar ta bi doka da tsari da kuma adalci wurin tabbatar da sauya fasalin ba tare da wani son kai ba.

Shehu ya kara da cewa bayan duba yanayin tattalin arzikin kasar, fasalin albashin 'yan siyasa da sauran masu rike da mukamai ya sauya da karin kashi 114.

Jirgin Tinubu Ya Sauka A Faransa, Ya Fadi Ranar Da Zai Dawo Najeriya

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyararsa ta farko zuwa kasar Faransa.

Shugaban ya kai wannan ziyarar ce don ganawa da manya-manyan shugabannin kasashen duniya.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron shi ne mai masaukin baki a taron da za a yi a birnin Paris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.