An Haɗa Faɗa: Ana Zargin Jigon APC da Tsaida Emefiele Takara Saboda a Yaƙi Tinubu
- Wasu shugabannin APC a Delta ba su hakura da rikicinsu da Ovie Omo-Agege ba har zuwa yau
- ‘Yan APC sun ce ‘dan takaransu ya daurewa Godwin Emefiele ya shiga takara a jam’iyyar APC
- Idan zargin gaskiya ne, Sanata Omo-Agege ya yi kokarin ganin Bola Tinubu bai samu tuta ba
Abuja - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Delta, ta zargi Ovie Omo-Agege da zama wanda ya ba Godwin Emefiele kwarin gwiwar neman yin takara.
Godwin Emefiele ya na cikin wadanda aka saye fam din takara da sunansu a APC, Punch ta ce ‘yan jam’iyya na zargin akwai aikin Omo-Agege.
Wasu daga cikin shugabannin APC sun aika wasika zuwa ga Bola Ahmed Tinubu, su na cewa Sanata Omo Agege ya zuga Emefeile ya nemi takara.
A cewarsu, tsohon mataimakin shugaban majalisar ya goyi bayan Gwamnan CBN saboda a hana Bola Tinubu samun takara a karkashin APC.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugabannin APC na reshen Ika a Delta; Michael Inana; Tom Onah; Nelson Ogharama da Michael Orunefe su ka sa hannu a wasikar da aka aika.
Inana da mutanensa su ka ce abin da Omo Agege ya aikata tamkar cin amanar APC ne.
Mr. Godwin Emefiele ya zama 'Dan APC
Rahoton ya ce ana zargin tsohon ‘dan majalisar ya yi amfani da taron 2022 da aka yi wajen mallakawa Mista Emefiele katin zama ‘dan jam’iyya.
Shugabannin na APC sun ce sun nunawa ‘dan siyasar hakan ba daidai ba ne domin bai dace a shigo da Gwamnan babban banki cikin takara ba.
Omo-Agege ya yi kunnen-kashi, ya gamsar da Emefiele ya kuma tabbatar masa zai hada-kai da Felix Morka domin ya taimaka ya samu tuta.
Masu korafin sun gabatar da wata jarida a matsayin hujjar yadda Mataimakin shugaban majalisar dattawan (a lokacin) ya shigo da Gwamnan APC.
Rahoton ya ce shugabannin APC na garin Ika da aka hada-kai da su domin ganin an cin ma nasara su ne Nduka Erikpume da kuma Hilary FadaIbude.
An kuma zargi ‘dan siyasar da bin ‘Yan Obidients saboda ya ci zaben Gwamna. Mutanen Omo Agege sun karyata zargin da wasikar ta kunsa.
Samuel Ortom da EFCC
Makonni uku bayan sauka daga karagar mulki sai ga Samuel Ortom a Hedikwatar EFCC a Makurdi, kamar yadda aka samu labari, an fito da shi.
Har yanzu Hukumar EFCC ba ta fadi dalilin aikawa Ortom goron gayyata ba, hadiminsa ya karyata rade-radin da ke yawo cikin makon nan.
Asali: Legit.ng