Kaduna: Uba Sani Ya Nada Tsohon Kwamishinan El-Rufai Shugaban KCTA
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya nada tsohon kwamishinan Nasiru El-rufai, Samuel Aruwan a matsayin shugaban KCTA
- Aruwan ya kasance tsohon kwamishinan tsaron cikin gida a tsohuwar gwamnatin Mallam Nasir El-rufai
- Gwamnan ya yi nade-naden mukamai da dama tun farkon hawanshi karagar mulki inda ya nada mafi yawan yaran Nasir El-rufai
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nada tsohon kwamishinan Nasiru El-rufai, Samuel Aruwan a matsayin shugaban Hukumar Kula da Birnin Kaduna (KCTA).
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa sakataren yada labaran gwamnan, Muhammad Shehu a ranar Talata 20 ga watan Yuni.
Aruwan shi ne tsohon kwamishinan tsaron cikin gida a gwamnatin El-Rufai
Mista Aruwan shi ne tsohon kwamishinan tsaron cikin gida a tsohuwar gwamnatin Nasiru Elrufai, Daily Nigerian ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar:
"Aruwan ya kammala digiri a fannin aikin jarida, ya shafe shekaru a bangaren aikin jarida kafin ya dawo aikin gwamnati a 2015.
"Yana kuma da kwarewa ta fannin dakile tare da gudanar da matsalar tsaro ta yanda ya dace."
Aruwan ya ba da gudumawa sosai a bangarori da dama a jihar
Sanarwar ta kara da cewa kamar yadda Leadership ta tattaro:
"Bayan ba da gudunmawa ta fannin kawo zaman lafiya a jihar Kaduna.
"Ya kuma ba da gudumawa wajen wayar da kan jama'a a bangaren ta'addanci da kuma 'yan fashin daji a Arewacin Najeriya."
Da yake taya shi murnanr samun wannan matsayi, Gwamna Uba Sani ya roki Aruwan da ya yi amfani da kwarewar da ya ke da shi wurin kawo ci gaba a hukumar KCTA.
Ya yi masa fatan alkairi da samun wannan matsayi, inda ya yi addu'ar ubangiji ya taimake shi.
Uba Sani Ya Nada Mukarraban Tsohon Gwamna El-Rufai Manyan Mukamai
A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa wanda ya hada da mukarraban tsohon gwamna.
Gwamnan ya nada mukarraban tsohon Gwamna Nasir El-Rufai manya-manyan mukamai a gwamnatinsa.
Sakataren yada labaran gwamnan, Muhammad Lawal Shehu shi ya sanar da nada wadannan mukamai, inda ya ce an duba kwarewa ce wajen nada mukaman.
Asali: Legit.ng