Jirgin Bola Tinubu Ya Sauka a Faransa, An Ji Ranar da Shugaban Kasa Zai Dawo Najeriya
- Shugaban Najeriya ya sauka a Faransa domin halartar taron tattalin arziki da za ayi a makon nan
- Jirgin da yake dauke da Bola Ahmed Tinubu ya tashi a filin Nnamdi Azikiwe da karfe 11:30 na safe
- Sababbin hafsoshin tsaro sun yi wa Tinubu rakiya, ana tsammanin dawowarsa gida a ranar Asabar
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya domin halartar babban taron da za ayi a birnin Faris da ke kasar Faransa.
Rahoton da aka samu daga tashar talabijin ta kasa watau NTA, ya tabbatar da cewa jirgin Bola Ahmed Tinubu ya kama hanyar Faransa.
Tinubu ya isa babban filin tashin jirgin saman Nnamdi Azikiwe ne da safiyar nan, da kimanin karfe 11:30 jirgin fadar shugaban kasa ya tashi.
Wannan taro da Mai girma Emmanuel Macron zai zama mai masaukin bakin shugabannin Duniya zai tattauna kan sha’anin tattali.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yaushe taron zai gudana?
Za a gudanar da taron ne a Palais Brongniart mai tsohon tarihi a ranakun Alhamis da Juma’a. Tawagar Tinubu za ta dawo gida a ranar Asabar.
Bidiyon da mu ka samu daga shafin Olusegun Dada a Twitter ya nuna an sauke tawagar shugaban kasar ne a jirgin sama mai saukar angulu.
Daga nan aka yi wa Tinubu rakiya zuwa cikin jirginsa, sai shi kuma ya yi sallama. A ‘yan rakiyan har da sababbin hafoshin tsaron da aka nada.
Mai taimakawa shugaban kasar wajen sadarwa da dabaru, Dele Alake ya ce mai gidansa zai samu halartar taron har ya sa hannu a yarjejeniyar.
Amfanin taron Faris
Punch ta ce ana sa ran zaman zai taimaka wajen jawo masu hannun jari, duba tasirin sauyin yanayi da kuma nazari a kan tasirin annobar COVID-19.
Jawabin da Alake ya fitar a ranar Talata ya ce masana tattalin arziki za su duba irin barnar da COVID-19 ta yi wa kasashe tare da kawo mafita.
Tinubu a kasar Faransa
A yammacin Talatar nan ne aka samu rahoto cewa jirgin fadar shugaban kasa ya isa Faransa dauke da Bola Tinubu da kuma wasu 'yan tawagarsa.
Da kimanin karfe 8:00 a agogon Najeriya, Shugaba Tinubu ya yi magana a shafukansa na sada zumunta, ya na tabbatar da ya isa lafiya.
Tun da ya hau mulki, Shugaban Najeriyan bai taba barin kasarsa ba. A baya an soki Muhammadu Buhari da yawan fita zuwa kasashen ketare.
Nadin Hafsoshi da Mukarrabai
A jiya aka rahoto Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya ce an canza hafsoshin tsaro, Sufetan 'yan sanda da shugaban kwastam.
Hadiza Bala Usman da Hannatu Musa Musawa sun samu mukamai. Za su rika Bola Tinubu shawara a kan al'adu da kuma tsare-tsaren gwamnati.
Asali: Legit.ng