Gwamnatin Tinubu Ta Dauko Batun Karin Albashi, An Kafa Kwamitoci Na Musamman
- Kungiyoyin ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa sun dawo kan teburin tattaunawa da gwamnatin tarayya
- Zaman da aka yi a Aso Rock a daren yau ya shafi yadda za a duba bukatun ma’aikata da 'yan kasuwa
- Hadimin shugaban Najeriya, Dele Alake ya ce tattaunawar ta haifar da kafa kwamiti na musamman
Abuja - A ranar Litinin, gwamnatin tarayya ta shaida cewa ta kafa wani kwamiti da zai duba jerin bukatun da kungiyoyin kwadago su ka gabatar.
Punch ta ce hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin fetur, wanda wannan ya jawowa jama’a karin wahala.
Kungiyoyin ‘yan kwadago su ka cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya a kan lamarin.
Bayan zaman na su, Mai taimakawa shugaban kasa wajen sadarwa da dabaru, Dele Alake da shugabannin ma’aikata sun yi wa ‘yan jarida bayani.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
NLC da TUC sun wakilci al'umma
Shugabannin kungiyoyin NLC da TUC; Joe Ajaero da Festus Osifo su ka wakilci ma’aikatan kasar.
Kamar yadda su ka shaidawa manema labarai a fadar shugaban kasa, an fitar da kwamitin da sauran kananun kwamiti za su gabatar masa da bukatu.
"Kowane bangare ya duba jerin da aka kawo, aka zakulo wadanda za a iya aiwatarwa. An raba wadannan abubuwa zuwa kashi uku –
Akwai wadada za a iya yinsu a nan-take; akwai wadanda za su dauki matsakaicin lokaci, sai wadanda za su dauki dogon lokaci kafin a cika.
Akwai wani kwamiti wanda zai zama kamar shi ke da akalar komai a hannunsa."
Matsayar 'yan kwadago bayan taron
Jaridar ta rahoto shugaban kungiyar ‘yan kasuwa, Festus Osifo ya na cewa gwamnati ta bada gudumuwarta, kuma daga yanzu za su rika yin aiki a tare.
Osifo ya ce kwamitin da Alake yake magana zai duba bukatum da aka gabatar kamar samar da motocin haya masu aiki da gas da batun karin albashi.
Joe Ajaero ya ce an soma aiki, ya na ganin kwamitocin za su iya kammala zama nan da makonni takwas.
An karya Naira a Najeriya
A baya an ji labarin yadda hamshakan masu kudin Najeriya sun karasa Biliyoyin Daloli tun da CBN ya saki arashin Naira a hannun 'yan kasuwa.
A lokacin da masana tattalin arziki su ke yabawa Bola Tinubu, lokacin wasu su ka tafka asara. Attajiran kamar su Aliko Dangote sun rasa Tiriliyoyi.
Asali: Legit.ng