Abba Gida-Gida Zai Tura ’Ya’yan Talakawa Karatu Kasar Waje, Gwamnati Ta Yi Tanadin Yadda Shirin Zai Tafi
- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana fara ba da gurbin karatu kyauta ga wadanda ke sha’awar zuwa karatun digiri na biyu
- Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara aiki a matsayin gwamnan ujihar ta Kano
- Ba wannan ne karon farko da gwamnatin Kano ke daukar irin wannan dama tana ba ‘yan jihar ba
Bayan karewar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje a jihar Kano, sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauko tafarkin tsohon gwamna Kwankwaso na tura ‘yan jihar karatu kasashen waje.
Wannan karatu dai zai zama a matakin digiri na biyu ne, wnada tuni aka bayyana hanyoyin da za a bi don samun gurbin wannan karatu, TRT Hausa ta ruwaito.
A wasu bayanai da gwamnati ta wallafa a shafinta na yanar gizo, an bayyana dalla-dalla matakai da ake bi don cire fom wannan dama ta karatu.
Wasu sharudda mai nema zai cika?
- Dole mai nema ya kasance dan asalin jihar Kano.
- Dole ya kammala digirin farko da sakamakon ‘first class’.
- Dole jami’ar da mutum ya yi digirin farko ta kasance sahihiya kuma amintacciya
- Dole ne a binciki lafiyar mai son wannan dama don tabbatar da zai iya karatu da ma tafiya zuwa wata kasa.
- Karshe, dole ne mai neman wannan tallafi ya cike fom din da gwamnati ta tanada a shafin yanar gizo
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta yaya ake cikawa?
Bayan tanadan abubuwan da ke sama, ana bukatar kowanne mai sha’awar cike fon din ya tabbatar takardunsa sun shirya, kuma yana da kwafinsu da zai iya turawa a shafin yanar gizo.
Hakazalika, ana sa ran kowanne mai nema zai cike fom din ne a wannan shafin nan ko kuma nan https://www.kanostate.gov.ng/scholarship_application.
Ba wannan ne karon farko da gwamnatin Kano ke irin wannan aikin ba, to amma abin tambayar; menene tasirin hakan? Kuma shin jami’o’in Najeriya sun gaza ne? Haka nan, abubuwan da za a karanta a waje babu shi ne a Najeriya?
Kwankwaso ya sake tura dalibai karatu a 2019
A wani labarin, kun ji yadda Kwankwaso ya sanar da ba da gurbin karatu kyauta ga ‘ya’yan talakawa a jihar Kano.
Ya bayyana hakan ne tare da bayyana sharuddan da za a cika don yin wannan aiki mai muhimmanci.
Ana yiwa Kwankwaso kallon mai tallafawa talakawa su yi karatu a kasashen waje, musamman a mulkinsa.
Asali: Legit.ng