Da dumi dumi: Kwankwaso zai tura yaran talakawa karatu zuwa kasashen waje

Da dumi dumi: Kwankwaso zai tura yaran talakawa karatu zuwa kasashen waje

Tsohon gwamnan jahar Kano, kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala shirin tura matasa masu sha’awar karo karatu zuwa kasashen waje domin cimma burinsu.

Legit.ng ta ruwaito hadimar Kwankwaso, Hajiya Binta Sipikin ce ta sanar da haka a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda tace gidauniyar Kwankwasiyya na gayyatar matasa masu son cigaba da karatu dasu garzayo domin samun tallafi kyauta.

KU KARANTA: Majalisa ta gayyaci shugaban kasa ya gurfana gabanta akan kashe kashen Zamfara

Da dumi dumi: Kwankwaso zai tura yaran talakawa karatu zuwa kasashen waje

Da dumi dumi: Kwankwaso zai tura yaran talakawa karatu zuwa kasashen waje
Source: Facebook

Sanarwar ta kara da cewa gidauniyar Kwankwasiyya ta bada wannan dama ne ga kowanne fannin ilimi, sai dai tana bukatar matasan da basu haura shekaru 30 bane kawai, kuma suke da digiri mai daraja ta farko, watau First Class.

Gidauniyar na kira ga wadanda suka cika wannan sharadi dasu aika takardar neman gurbin karatun da takardunsu zuwa ga babban daraktan gidauniyar Kwankwasiyya dake gidan Kwankwasiyya, titin Lugarda, cikin unguwar Nassarawa Kano.

Ana bukatar duk masu neman wannan dama dasu mika duk abubuwan da ake bukata cikin kwanaki goma sha hudu, daga cikin takardun da zasu mika akwai shaidar kammala digiri, takardar haihuwa, da dai sauransu.

A wani labarin kuma hadimin shugaban kasa akan harkar samar da ayyuka ga matasa, Afolabi Imoukhuede ya tabbatar ma matasan dake cin gajiyar tsarin daukan aiki na gwamnatin tarayya na N-Power cewa zasu sau albashinsu na watan Maris cikin satin nan.

Afolabi ya bada wannan tabbaci ne a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, yayin da yake musanta zargin da wasu ke yi na danganta nukusanin biyan albashin ga dabarar dakatar da biyan N-Power gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel