Gajerun Bayanai a Kan Mutane 8 da Tinubu Ya Nada a Matsayin Masu Bada Shawara

Gajerun Bayanai a Kan Mutane 8 da Tinubu Ya Nada a Matsayin Masu Bada Shawara

  • Bola Ahmed Tinubu ya sanar da wasu mutanen da za su yi aiki da shi a matsayin masu bada shawara
  • Shugaban Najeriyan ya yi nadin ne bayan majalisar tarayya ta amince masa zakulo mukarabbai
  • Daga cikin wadanda za su yi aiki da Tinubu har da wani Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari

Abuja - Legit.ng Hausa ta bi diddikin sababbin masu ba Shugaba Bola Ahmad Tinubu shawara, ta dauko kadan daga cikin tarihin rayuwarsu.

1. Nuhu Ribadu

Abin da aka fi sanin Nuhu Ribadu da shi, shi ne kasancewa shugaban EFCC na farko. Tsohon ‘dan takarar shugaban kasar ya yi karatu a ABU da kasar waje.

Lauyan wanda ya kai matakin AIG a aikin ‘dan sanda ya yi suna ne a dalilin Olusegun Obasanjo, ya kuma yi aikin kwamitin PRSTF a shekarar 2012.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

Shugaban kasa
Bola Tinubu a kujerar Shugaban kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Dele Alake

Kafin zama Mai bada shawara a yau, Dele Alake ya yi wa Bola Tinubu kwamishinan yada labarai da dabaru tsakanin 1999 da 2007 da ya na Gwamnan Legas.

Alake ya yi aiki tare da ubangidan Tinubu watau Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ya na cikin ‘yan kungiyar editoci da na 'yan jarida a Najeriya.

3. Wale Edun

Wale Edun kwararren masanin tattalin arziki ne wanda ya goge a aikin banki, ya yi digirinsa na farko da na biyu a ilmin tattalin arziki a Landan da Sussex.

Daily Trust ta ce Hadimin ya yi aiki a bankunan kasashen wajea shekarun 1980s kafin kafa bankinsa a gida wanda yanzu ya koma Stanbic IBTC Plc.

4. Olu Verheijen

The Cable ta ce Olu Verheijen ta shafe sama da shekaru 20 a harkar aikin gas da makamantansu a Afrika, yanzu ita ce shugabar kamfanin Latimer Energy.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan PDP Ya Zama Babban Mai Yabon Gwamnatin Tinubu Dare da Rana

Bayan kasancewarta mai ba kamfanin Energy for Growth Hub shawara, Verheijen ta kafa gidauniyar BFA Foundation, tayi digiri biyu daga jami'o'in Amurka.

5. Zacch Adedeji

Rahoto daga Economic Confidenital ya nuna cewa Zacch Adedeji ya yi Kwamisihinan kudi a Oyo, bayan nan ne ya zama shugaban hukuma NSDC.

Adedeji kwararren Akanta ne wanda ya san ilmin cigaban tattalin arziki da haraji, ya gama jami’ar OAU da mafi darajar digiri, daga nan ya tsallaka kasar Amurka.

6. Salma Anas-Kolo

Mai bada shawara a kan kiwon lafiya, Salma Anas-Kolo Kwamishina ce a gwamnatin Kashim Shettima. Bayanan shafinta sun nuna ta kware a sha'anin lafiya.

Baya ga kasancewa wanda ta san ciwon mata, Salma Kolo ta kafa cibiyoyin taimaka masu Rahoton ya ce mahaifinta ya taba yin mataimakin Gwamna a jihar Borno.

7. Yau Darazo

Ya’u Darazo shi ne mai ba Muhammadu Buhari shawarwari na musamman da ya na ofis. Asalinsa mutumin Darazo ne daga Bauchi, yana cikin masoyon Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Suka Hana Abdulaziz Yari Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

A wani rahoto da aka taba fitarwa, an fahimci tun ya na aiki da shugaba Buhari, Darazo ya na cikin masu goyon bayan Tinubu ya samu tikiti, ya lashe zaben 2023.

8. John Uwajumogu

Mai bada shawara a kan harkar kasuwanci, hannun jari da masana’antu shi ne John Uwajumogu wanda ya yi fiye da shekaru 20 ya na irin wannan aiki a Duniya.

Baya ga digirin farko, bayanan da mu ka samu ya nuna Uwajumogu ya na da digiri a harkar huldatayyar kasashe daga jami’ar Tuff, ya yi aiki har a irinsu PWC.

Okowa da hukumar EFCC

Rahoton da mu ka samu shi ne Edwin Clark ya ce daga shekarar 2007 zuwa 2022, an aikowa gwamnatin jihar Delta da N1.7tr a matsayin kason arzikin danyen mai.

Da aka nemi jin ina Ifenayi Okowa ya kai dukiyar, sai ya ce ya biya ‘yan fansho Naira Biliyan 5 a lokacinsa. Wannan ya jawo Clark ya kai karar tsohon Gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng