Abdulrasheed Bawa: Dalilai 2 Da Ake Zato Suka Sa Tinubu Dakatar Da Shugaban EFCC Daga Mukaminsa

Abdulrasheed Bawa: Dalilai 2 Da Ake Zato Suka Sa Tinubu Dakatar Da Shugaban EFCC Daga Mukaminsa

  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa a watan Faburairu ta shekarar 2021
  • Bawa mai shekaru 43, ya kasance shugaban hukumar EFCC mafi karancin shekaru da ake ganin ba a taba samun kamarsa ba a tarihin hukumar
  • A ranar Laraba 14 ga watan Yuni, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Bawa a matsayin shugaban hukumar inda ya umarci a bincike shi

FCT, Abuja - Bayanai sun bayyana dalilin da yasa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa.

Bawa, mai shekaru 43, ya kasance a kan kujerar hukumar tun a watan Faburairu ta shekarar 2021 da tsohon shugaban kasa Buhari ya nada shi.

Tinubu ya dakatar da Bawa bisa dalilai guda 2
Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar EFCC Daga Mukaminsa. Hoto: EFCC/Bola Tinubu.
Asali: Facebook

1. Rawar da ya taka game da sauya fasalin Naira ya harzuka Tinubu

Kara karanta wannan

EFCC Ta Sanar da Sabon Shugaban Rikon Kwarya Bayan Tinubu Ya Dakatar da Bawa

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa a ranar Laraba 14 ga watan Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban har ila yau, ya umarci da ayi kyakkyawan bincike akan shugaban lokacin da yake jagorantar hukumar.

Kafin yanke wannan hukunci, Tinubu ya gana da Bawa a watan Mayu, cewar The Guardian.

Daily Trust ta tattaro cewa Tinubu ya dakatar da Bawa ne bisa zargin taka muhimmiyar rawa wajen sauya fasalin Naira da ya jefa mutanen Najeriya a cikin mawuyacin hali.

Tinubu na zargin sauya fasalin Naira a kasar, an kirkiro ta ne don kawo cikas da kuma hana shi cin zabe na shugaban kasa.

2. Matsalar da ke tsakanin Bawa da Matawalle

Dalili na biyu shi ne yadda Bawa ke zargin tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle kan badakalar makudan kudade.

Kara karanta wannan

Daga Ribadu Zuwa Olukoyede: Jerin Sunayen Shugabannin EFCC Da Jihohi/Yankunansu

Yayin da tsohon gwamnan ya zargi Bawa da neman cin hanci har na $2m daga hannunsa, inda Bawa ya musanta zargin.

Legit.ng ta tattaro cewa yanzu haka Bawa na hannun Hukumar 'Yan Sandan Farin Kaya (DSS) yana amsa tambayoyi.

ShugabaTinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya amince da dakatar da shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Willie Bassey a ranar Laraba 14 ga watan Yuni.

Sanarwar ta ce dakatarwar na da alaka da zarginsa da ake masa na badakalar makudan kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.