Kalaman El-Rufai Sun Jawo Kungiya Ta Bukaci Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Gwamna

Kalaman El-Rufai Sun Jawo Kungiya Ta Bukaci Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Gwamna

  • International Society for Civil Liberties and Rule of Law ta fito ta soki Malam Nasir El-Rufai
  • Kungiyar ta na so a cafke tsohon Gwamnan Kaduna, ta zarge shi da fifita Musulunci a Najeriya
  • Shugaban Intersociety, Emeka Umeagbalasi ya ce El-Rufai ya murkushe kiristocin Jihar Kaduna

Owerri – Wata kungiya International Society for Civil Liberties and Rule of Law da aka fi sani da Intersociety ta na so a damke Malam Nasir El-Rufai.

Kamar yadda rahoto ya fito daga jaridar Vanguard a yau,kungiyar ta zargi tsohon Gwamnan jihar Kaduna da goyon bayan a musuluntar da Najeriya.

Intersociety ta ce Nasir El-Rufai ya na kira da aka kafa mulkin musulunci a Najeriya, wanda ke garaye da sauran Mabiya addinan da ba musulunci ba.

El-Rufai
Nasir El-Rufai da zai bar ofis Hoto: @MuyiwaAdekeye
Asali: Twitter

Shugaban wannan kungiya, Emeka Umeagbalasi ya zanta da manema labarai a garin Owerri a jihar Imo, inda ya jero wasu zunuban tsohon Gwamnan.

Kara karanta wannan

Hukuma Sai Lallashi: Gwamna Ya Karbe Filin da Aka Ba Jami’ar Janar Ibrahim Babangida

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mista Emeka Umeagbalasi ya jefi Malaman El-Rufai da neman jawo rikici tsakanin jama'a da kisan kare dangi da laifin tunzura al’umma da kalamansa.

Wannan kungiya mai neman tabbatar da bin doka ta ce tun ba yau ba ta ke jan hankali game da tsohon Ministan, sai a yanzu maganar ta fito fili.

"A wani faifen murya ko bidiyo, tsohon Gwaman Kaduna ya na kurin nasarar maida Kaduna kasar musulunci ta hanyar cigaba da rike mulki tun 2015.
An maimaita irin haka a Najeriya ta hanyar tsaida tikitin Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa.
Intersociety ta saba bayyana irin yankan ragon da ake yi wa mutanen Kudancin Kaduna da Benuwai, Filato, Nasarawa, Kogi, Neja, Taraba da Adamawa."

- Emeka Umeagbalasi

Menene hujjojin kungiyar?

Rahoton ya ce Umeagbalasi ya yi ikirarin a shekarun nan, an hallaka mutane a Kudu maso yamma da Kudu maso gabashin Najeriya saboda bambancin addini.

Kara karanta wannan

Muna zuba muku ido: Kungiyar Islama ta ce za ta barranta da 'yan siyasar da ba sa amfanar Musulmai

Legit.ng Hausa ta fahimci babu inda kungiyar nan ta Intersociety ta bada gamsassun hujjojin da ke tabbatar da irin kashe-kashen da yake cewa ana yi yankunan.

Intersociety ta ce a 2015 El-Rufai ya hana Kirista tikiti a zaben Gwamna, amma bincike ya nuna mataimakin Gwamnan jihar Kaduna a lokacin kirista ne.

Binciken Gwamnan CBN

Da alama Godwin Emefiele ya shiga uku domin an ji labari DSS ta karbe takardunsa domin hana shi barin Najeriya, kuma ana shirin a binciki inda yake zama.

Dakataccen Gwamnan na CBN bai isa ya je ko ina ba, hukuma ta taso shi a gaba da bincike. Ana tunanin za a gayyaci Darektocin bankin ayi masu tambayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng