An Tsinci Gawar Wani Ango Da Amaryarsa Mai Juna Biyu A Cikin Gidan Su A Abuja

An Tsinci Gawar Wani Ango Da Amaryarsa Mai Juna Biyu A Cikin Gidan Su A Abuja

  • Al'ummar babban birnin tarayya Abuja sun tsinci kansu cikin wani yanayi bayan wayar gari da suka yi da labarin mutuwar wani miji da matarsa
  • Ana zargin guba aka sanyawa ma'auratan a cikin abinci inda suka ce ga garinku bayan sun sha murkususu ba tare da agaji ba
  • Lamarin ya afku a safiyar Asabar, 10 ga watan Yuni kuma matar ma na dauke da juna biyu

A wani yanayi mai cike da bakin ciki, an gano gawar wani magidanci da amaryarsa wacce ke dauke da juna biyu a gidansu da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wani mai amfani da shafin Twitter mai suna Salim Sani shine ya sanar da labarin mutuwar mutumin wanda ya bayyana a matsayin dan uwansu.

A cewarsa, an tsinci gawar Hussaini Lawan da matar tasa ne a safiyar ranar Asabar, 10 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Kawo hujja: 'Yan sanda sun karya tsohon gwamna Matawalle kan zargin sun masa sata a gida

Miji da matar da suka rasu a gidansu
An Tsinci Gawar Wani Ango Da Amaryarsa Mai Juna Biyu a Cikin Gidan Su a Abuja Hoto: @SaliimSanii
Asali: Twitter

Salim ya rubuta a shafin nasa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“innalillahi wainna ilaihi rajiun, an gano dan uwanmu hussaini lawan & matarsa a mace a gidan aurensu a safiyar yau. Don Allah ku saka su a kyawawan addu’o’inku, Allah SWT ya yafe masu kura-kuransu sannan ya sa su a aljannatul firdaus. aameen.”

Wani mai amfani da Twitter, Sulaiman Yusuf ya bayyana cewa marigayin abokin aikinsa ne a baya.

Ya rubuta:

”Innallahihi wainnna ilaihi rajiun. Na samu labarin kimanin awanni 2 da suka wuce...mun yi aiki tare da shi a zone 4 plaza Abuja” Za a yi Janaza nan da awa 1 a nan hanyar Suleja kaduna. Allah ya sa su a Al-Jannah.”

Har ila yau, wata matashiya da ake zaton tana da nasaba da mamatan mai suna Farida Lawal, ta saki wani bidiyo inda ta yi karin haske game da abun da ake zargin ya kashe su.

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: 'Yan Bindiga Sun Halaka Fitaccen Malami a Babban Birnin Jihar PDP

Kamar yadda ta bayyana a bidiyon, ta ce an sanya masu guba ne a cikin abincin da suka ci, inda ta ce an gano su kwance dumu-dumu cikin aman jini da suka yi sannan ga sauran abincin da suka ci a gefe.

Ga bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@HananColections ta yi martani:

"Kai. ? Innalillahi Wa Inna Ilaihirrajiun "

@mss_mienarh_ ta ce:

"Innalillahi wa inna ilayhi rajiun! Allah yayi musu rahama."

@Minikabo ya ce:

"Innalillahi wa inna ilaihir rajeoun. Allah ya basu aljannar firdousi."

@marieyrm ta ce:

"Inna Lillahi Wa Inna Ilyhee Rajeeun ☹️ Allah ya gafarta masu ya Rahma masu ya sa Aljannah Firdausi makomar su.."

Yan bindiga sun farmaki al'ummar Neja, sun kashe manoma 50

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun kai mummunan hari kan garuruwa a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Maharan sun halaka manoma kimanin su 50 a hare-haren da suka kai kan kauyaka daban-daban a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng