‘Yan Bindiga Sun Yi Ta’adi a Arewa, Sun Kashe Attajiri, Dauke Sarakunan Gargajiya
- ‘Yan bindiga sun sake komawa garin Ningi a jihar Bauchi, wannan karo sun kashe ‘dan kasuwa
- Bayan gawar ‘dan kasuwar da aka tsinta, an tabbatar a miyagun sun yi garkuwa da wasu Sarakai
- Mai garin Bakutunbe da Hikimin Balma sun shiga hannu, an ce sai an biya N8m a kan kowanensu
Bauchi - Wasu da ake zargin miyagun ‘yan bindiga ne sun shiga karamar hukumar Ningin jihar Bauchi, su ka yi gaba da Hakiman wasu garuruwa.
Premium Times ta ce Sarakan da aka dauke su ne na Bakutunbe da Balma, ana zargin an yi garkwa da su a ranar Asabar, ana neman kudin fansa.
Baya ga Sarakan da su ka fada hannun ‘yan bindigan, sun kuma kashe wani shahararren ‘dan kasuwar yankin da aka fi sani da Haruna Dan-Oc.
'Yan bindiga sun shigo cikin dare
Wani mazaunin garin da ya boye sunansa saboda barazanar tsaro ya shaida cewa gungunan miyagun sun auko Balma ne da karfe 11:00 na dare.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa ‘yan bindigan sun buda wuta kafin su dauke Hakimin garin, su yi awon gaba da shi.
Bayan ‘yan bindigan sun tsere aka tsinci gawar Dan OC a kwance a kasa da harsashi a cikin kansa, ko da aka je babban asibitin Ningi, sai aka ce ya mutu.
An sace Mai garin Bakatunbe
Rahoton Punch ya ce a daren ne kuma wadannan miyagun ‘yan ta’adda su ka shiga Bakutunbe, su ka dauke mai garin kauyen, Ya’u Gandu mai shekara 45.
‘Yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan takwas domin a iya karbar fansar kowane daga cikin wadannan Bayin Allah da aka yi garkuwa da su.
Shugaban karamar hukumar Ningi, Ibrahim Zubairu ya tabbatar da haka ga manema labarai a jiya.
Dole a dauki matakin gyara tsaro
Shugaban karamar hukumar Ningi ya ce zai kyau a aiko masu da sojoji domin su kare al’umma, tare da kira ga mazauna yankin su dage da addu’o’i.
An nemi jin ta bakin Muhammed Wakili wanda shi ne Kakakin Rundunar ‘yan sandanBauchi, amma ba ayi nasarar samun wayoyin salulansa ba.
Rikicin siyasa a Benuwai
Rahoto ya zo cewa Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia ya ce babu abin Samuel Ortom ya bari sai bashin N180bn, ya ce ko mota daya bai samu a ofis ba.
Gwamna Ali ya ce ya gaji bashin albashi wata da watanni na ma’aikatan gwamnati, sannan ya koka da cewa an yi shekaru biyu ba a biya fansho a jihar ba.
Asali: Legit.ng