Tinubu Ya Rattaba Hannu a Kudirin Farko Da Ya Zama Doka a Zamaninsa
- Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin da watakila shi ne na farko da ya ci karo da shi
- Kudirin canza shekarun ritayar Alkalan Najeriya ya zama doka, sai Alkali ya shekara 70 zai bar aiki
- A watan Mayu aka kai kudirin zuwa fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai sa hannu a kai ba
Abuja - A ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni 2023, rahoto ya zo cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya tsawaita shekarun aikin Alkalai.
Jaridar The Cable ta fitar da labari cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince ya sa hannu wajen karawa Alkalai shekarun ritaya.
Bayan rattaba hannu a kan wannan kudiri dazu, shekarun da Alkalin kotu za su ajiye aikinsu ya zama daya, babu bambanci tsakaninsu.
Buhari ya ki sa hannu
Kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis, majalisa ta gabatar masa da wannan kudiri da zai sa masu shari’a su kara dadewa a bakin aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa Abubakar Malami SAN ne ya ba shugaban Najeriya na lokacin shawarar ya yi watsi da kudirin, kuma haka aka yi.
Bayan Tinubu ya shiga ofis ya ci karo da kudirin da ya samu amincewar duka ‘yan majalisar tarayya, sai ya ga bukatar ya yi aiki a kai.
Shekaru 65 zuwa 70
Da wannan mataki da sabon shugaban na Najeriya ya dauka, shekarun ajiye aikin Alkalai ya canza daga shekaru 65 da aka sani a doka.
Duk wani Alkali zai shafe shekaru 70 kafin ya yi ritaya, a baya Alkalan kotun koli ne kadai su ke da damar kai wannan shekaru a bakin aiki.
Sai dai hakan zai yi tasiri wajen kudin da ake kashewa bangaren shari’a, kuma zai canza yadda za a rika samun karin girma a kotun kasar.
Kudirin ya daidaita Alkalan kotun koli da Alkalan kotun tarayya, kotun daukaka kara, manyan kotu, kotun majistare da na kotun shari’a.
An kawo wannan gyara ne bayan an yi garambawul ga wani sashe na kundin tsarin mulki kamar yadda doka ta ba ‘yan majalisar tarayya iko.
Siyasar Majalisar Tarayya
Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa watau Idris Wase da Aminu Jaji sun ki yarda su hadu da Bola Ahmed Tinubu a kan batun takarar da suke yi.
An ji labari a daren yau ne Shugaban kasa ya yi zama da 'yan majalisa, ya nemi su goyi-bayan takarar Godswill Akpabio da kuma Tajuddeen Abbas.
Asali: Legit.ng