Tsadar Kifi: Farfesa Ya Shawarci 'Yan Najeriya Su Rungumi Kiwon Kwadi
- Wani Farfesa a jami’ar Ilorin, Moshood Mustapha ya bayyana yadda ake samun alkairi da karuwar arziki a kiwon kwadi
- Farfesan ya bayyana haka ne yayin gabatar da wata lakca a ranar Alhamis 8 ga watan Yuni a Ilorin babban birnin jihar Kwara
- Ya ce ganin kifi ya yi tsada da kuma yadda wasu dabbobi da kwari ke cinye kwadi dole ne a samar da yanayi mai kyau don kiwata su
Jihar Kwara – Farfesa Moshood Mustapha na tsangayar ilimin halittar dabbobi a jami’ar Ilorin da ke jihar Kwara ya kirayi ‘yan Najeriya akan kiwon kwado don karuwar tallalin arziki.
Farfesan ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis 8 ga watan Yuni a yayin gabatar da lakca a Ilorin babban birnin jihar Kwara.
Ya bayyana cewa yadda kifi ya yi tsada da kuma yadda wasu dabbobi ke cinye kwadi, shi yasa ya zama dole a ci gaba da kiwon kwadi, cewar Daily Nigerian.
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mun yi shawarar duba bangaren kiwon kwadi tun daga farkonsu har lokacin da za su girma.
“Tun da kwadi suna rayuwa ne a ruwa, samun nasarar kiwon ta danganta da yadda aka inganta harkar ruwa da kuma samar da shi.
Farfesan ya bayyana irin abincin da kananan kwadi ke bukata
Farfesan yace kananan kwadi ana ciyar da su ne daga ganyen gwanda da kwari a cikin ruwa da kuma kifi.
Ya kara da cewa, kananan kwadin za su samu ingantacciyar rayuwa idan suna samun irin abincin da suke so da kuma samun tsaftataccen ruwa.
An bukaci gwamnati da masu ruwa da tsari kan inganta harkokin noma
Har ila yau, masana sun bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su samar da hanyoyi don tabbatar da kare kifi musamman a tafkunan da ake da su a kasar.
Sun tabbatar da cewa wannan hanya za ta samar ingantattun tafkuna da kuma kiyaye kiwon kifi don wadatar mutane a wannan lokaci da mutane suka fi bukararsu.
Tashin Kayan Masarufi Nasa Wasu Magidanta Tsallake Cin Abincin Rana ko Na Safe
A wani labarin, Yadda farashin kaya ke kara tashi kullum a Najeriya ya sa wasu gidaje tsallake cin abinci a wani lokaci.
Mafi akasari hakan na faruwa ne saboda ambaliyar da aka samu wadda ya yi sanadiyyar lalacewar gonaki.
Asali: Legit.ng