Ga Irinta Nan: Masu Kwacen Waya 2 Sun Gamu da Hukunci Mai Tsauri Bayan Kawo Su Gaban Alkali a Kano

Ga Irinta Nan: Masu Kwacen Waya 2 Sun Gamu da Hukunci Mai Tsauri Bayan Kawo Su Gaban Alkali a Kano

  • Yayin da ake ci gaba da kamo masu satar waya, alkalai na ci gaba da aikinsu na daure mai laifi a jihar a Kano
  • An gurfanar da wasu matasa biyu bisa zarginsu da yin fashi da makamin waya, wanda tuni suka amsa laifin da suka aikata
  • Ya zuwa yanzu, gwamnatin Kano ta ce duk wanda aka kama da laifin satar waya kallon dan fashi da makami take masa

Jihar Kano - Wata kotun shari’ar musulunci a jihar Kano da ke zamanta a Kofar Kudu karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ta yanke wa wasu masu faucen waya, Walid Adamu da Haruna Abubakar hukuncin daurin shekara daya a gidan yari.

An gurfanar da tsagerun biyu a gaban kuliya ne bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi fashi da makami da kuma satar waya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

An same su da laifin kai hari kan wani Abubakar Muhammad da ke unguwar Samegu a karamar hukumar Kumbotso a lokacin da ya je masallaci domin yin sallar Asuba.

Yadda aka daure masu satar waya
Taswirar jihar Kano a Arewa maso Yamma | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Bayan an karanta musu tuhume-tuhumen, sun amsa laifinsu, wanda daga nan aka yanke musu hukuncin da ya dace dasu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda masu kwacen waya suka addabi jama'ar Kano

Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya na yawan fama da matsalar masu satar waya, musamman a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan.

An sha samun lokuta daban-daban da 'yan ta'addan ke satar waya tare da jikkatawa ko ma hallaka mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Wannan ne ma yasa gwamnatin jihar ta ayyana cewa, yanzu za a ke yiwa duk wani dan kwacen waya kallon dan fashi da makami.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Waiwayo Kan Masu Kwasar Ganima, Kusan Mutum 50 Sun Shiga Gagarumar Matsala a Kano

Wannan na nufin, za a ke yiwa masu kwacen wayan hukuncin da ake yiwa wadanda aka kama da laifin fashi da makami kamar yadda dokar jihar ta tanada.

An gurfanar da DJ da ya addabi daliban Islamiyya da tsananin kida

A wani labarin, kunji yadda aka gurfanar da wani matashi mai sana'ar kade-kade bayan da ya addabi daliban makarantar Islamiyya da kida mai tsanani.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, an ce matashin ya yi kunnen kashi a lokacin da aka yi masa magana kan kure sauti a kusa da makarantar Islamiyyan.

Alkali ya umarci a ajiye shi har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari'ar a nan gaba kadan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.