Yaro Ya Sheka Barzahu Wajen Satar ‘Ganima’ a Wurin da Gwamnatin Kano Ta Ruguza
- Wani matashi ya je inda gwamnatin Kano ta ruguza a filin idi domin sato kayan da suka rage a ginin
- Bayan ya kinkimo rodi da wasu kaya ne sai mota ta buge shi, a nan wannan yaro ya gamu da ajalinsa
- Akwai wasu mutanen da yawa da su ka samu rauni a sakamakon fadowar gini yayin da suka je sata
Kano - An samu rahoto cewa babbar mota ta hallaka wani yaro yayin da wasu da-dama su ka jikkata a wani filin idi da yake garin Kano.
Abin da ya faru kuwa kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto shi ne wadannan mutane sun nemi daukar kaya a wurin da aka ruguza.
Wasu ‘yan iskan gari su na satar ragowar kayan da aka bari bayan an rusa gine-gine, a irin haka ne yaron nan ya rasa ransa a jihar Kano.
Wani wanda abin ya faru a gabansa, ya shaidawa jaridar cewa yaron ya na kokarin daukar rodi da kofofi ne sai wata babban mota ta buge shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ko da motar ta buge wannan yaro, ko shurawa bai sake yi ba, nan ta ke ya yi sallama da Duniya.
Yadda abin ya faru - Shaida
"Mu na tsaye a nan sai yaron da wasu su ka fito dauke da fallen kwano, karfen rodi da kofofi. Ba mu san wanene ya biyo su ba.
Su na da matukar yawa, amma da yake shi kwanakinsa sun kare, sai wata tirela ta auka masa, ta na bi ta kansa kuwa sai ya mutu.”
- Mai bada shaida
Rahoto ya ce akwai wani wanda aka yi tunanin ya hallaka bayan sato kayayyakin, haka zalika an tabbatar da cewa da-dama sun samu rauni.
Abin da ya faru kuwa shi ne a lokacin da wadannan matasa su ke kokarin satar rodi daga sashen da aka ruguza, sai ragowar ginin ya duro masu.
'Yan sanda sun cafke wasu
Abdullahi Haruna Kiyawa wanda shi ne kakakin jami’an ‘yan sandan reshen jihar Kano ya ce sun cafke mutane 49 da ake zargi da satar ‘ganima’.
Abdullahi Kiyawa ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar karbe wasu kofofi da tagogin zamani, na’urorin AC hudu da guduma da mutane su ka dauke.
Maganar Sheikh Ishaq Adam Ishaq
Ana da labari mutane su na ta tsoma baki a kan irin ruguza wurare da Gwamnatin Abba Kabir Yusuf take yi, har malaman addini sun yi magana.
Sheikh Barr. Ishaq Adam Ishaq ya yi bayanin hanyoyin karbe filaye a dokar kasa, shehin ya ce ba haka nan Gwamna zai raba mutum da filinsa ba.
Asali: Legit.ng