Gasar Jima’i a Sweden: Shehu Sani Ya Yi Fatali Da Gasar, Ya ce Najeriya Ba Ta Bukata

Gasar Jima’i a Sweden: Shehu Sani Ya Yi Fatali Da Gasar, Ya ce Najeriya Ba Ta Bukata

  • Tsohon sanata a jihar Kaduna, Shehu Sani ya yi gargadi da kada a kawo wa Nahiyar Afirka sabuwar gasar jima’i da aka kirkira a kasar Sweden
  • Sanatan ya yi wannan gargadi ne a shafinsa na Twitter yayin da yake mai da martani game da gasar da kasar Sweden ta kirkiro a kwanan nan
  • Ya ce wasannin da kwamitin shirya wasannin Olympics ya amince da su kadai sun isa, ba sai an kawo wani sabon abu ba zuwa kasar

Jihar Kaduna – Tsohon sanata a jihar Kaduna, Shehu Sani ya gargadi mahukunta a Najeriya da kada su kuskura su kawo gasar jima’a da za a fara a kasar Sweden zuwa Najeriya.

Sanata Shehu Sani ya yi wannan gargadi ne yayin mai da martini a shafinsa na Twitter a ranar Talata 6 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Ƙara Albashi, Ya Rage Ranakun Zuwa Aiki Saboda Tashin Kudin Man Fetur

Shehu Sani ya yi gargadi mutane kan shigo da gasar jima'i Najeriya
Shehu Sani Ya Gargadi Mutane kan Gasar Jima'i. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Ya ce wasannin da kasashe suka aminta da su na kwamitin Olympics kadai sun isa a Najeriya, don haka ba a bukatar sabuwar gasar jima’i da kasar Sweden ta kawo.

A gobe Alhamis ne za a fara gasar a Sweden

Vanguard ta tattaro cewa a ranar Lahadi 4 ga watan Yuni kasar Sweden ta kaddamar da fara gasar jima’i a na farko a Nahiyar Turai wadda za a fara a gobe Alhamis 8 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar cewa masu gasar jima’in za su na yi kullum wanda zai dauki tsawon sa’a guda kadai.

Shehu Sani ya gargadi mutane akan kawo gasar Najeriya

A cewarsa:

“Kada ku kawo mana sabuwar gasar jima’i na kasar Sweden zuwa Nahiyar Afirka. Wasannin da muke yi wadda kwamitin Olympics na kasa da kasa na amince da su ya ishe mu."

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba

Shugaban gasar na jami’i a kasar Sweden, Dragan Bratych ya ce yaso ace gasar ta samu karbuwa a duniya baki daya ta yadda za a dauketa kamar sauran wasanni.

Sweden Ta Halasta Jima’i a Matsayin Daya Daga Wasannin da Ake Yi a Kasar

A wani labarin, kasar Sweden ta halasta gasar yin jima'i a Nahiyar Turai inda ta shirya don fara gasar a mako mai zuwa.

Rahotanni sun tabbatar cewa wadanda za su gwabza a gasar za su kwashe tsawon sa'o'i shida a kowace rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel