Batun $53m: Bayan Saukan Buhari, Asirin Gwamnan CBN Ya Tonu, An Tura Masa Sammaci
- Babbar lotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci gwamnan babban bankin Najeriya, CBN ya gurfana a gabanta
- Mai Shari’a, Iyang Ekwo ne ya bayyana hakan a ranar Talata inda ya bukaci Emefiele ya mutunta gayyatar kotun
- Ana zargin Emifiele da karkatar da wasu kudaden Paris Club, yayin da ya sake $17m a madadin $70m na makudan kudaden
FCT, Abuja – Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godswill Emefiele ya yi Karin haske kan kudi $53m na Paris Club.
Mai Shari’a, Iyang Ekwo a ranar Talata ya bayyana cewa dole Emefiele sai ya halarci gayyatar kotun.
Ana zargin Emefiele da sake $17m kadai a madadin $70m na bashin da ba a biya ba, wadda hakan ke nufin akwai sauran $53 da ba a sake su ba.
Tun shekarar 2020 ake shari'a kan kudi
A watan Janairu ta shekarar 2020, kotun ta umarci Emefiele ya gurfana a gabanta don biyan sauran kudin har $53m, da kuma bayyana dalilinsa na rike sauran kudin da zai iya hana shi zuwa gidan gyaran hali, cewar TheCable.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka a watan Oktoba na shekarar 2020, lauyoyin Joe Agi, Isaac Ekpa da Chinonso Obasi sun kai karar CBN da ministan kudi da kuma kamfanin Linas inda suka suka bukaci babban Sifetan ‘yan sandan Najeriya ya sa a kama Emefiele kan kudin Paris Club.
Leadership ta tattaro cewa kotun ta karbi korafin inda ta umarci Emefiele ya gabatar da kansa a gabanta a ranar Laraba 18 ga watan Janairu, har ila yau, kotun ta dage sauraran karar zuwa watan Maris na shekarar 2020.
A wata karar ranar 12 ga watan Janairu da Emefiele ya daukaka ya bukaci kotun ta ajiye umarnin da ta bayar na gurfanar da shi a gabanta akan kudin Paris Club har $53m.
Kotun ta ce dole Emefiele ya gurfana a gabanta
Mai Shari’a, Ekwo a martaninsa, ya ce kotun ba za ta amince da wani tsari ba har sai Emefiele ya gurfana a gaban kotun.
A cewarsa:
“Ba na bukatar jin wani abu akan wannan korafin har sai Mista Emefiele ya gurfana a gaban wannan kotun.
“Don haka, zan ba ku ranar da za ku sake dawo wa kotu da kuma bin umarnin da kotun ta bayar.”
An dage ci gaba da sauraran karar zuwa 19 ga watan Yuli na wannan shekara.
Emefiele Ya Shiga Tasku, Gwamna Matawalle Ya Aike da Sako Ga Buhari
A wani labarin, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya roki shugaban kasa, Buhari da kada ya bar Godswill Emefiele ya fice daga kasar.
Gwamnan ya roki Buhari ne da kada ya bar Emefiele ya fita kasar ketare don karu karatu makwanni kadan kafin rantsar da sabuwar gwamnati.
Asali: Legit.ng