Gwamna Ya Ƙara Albashi, Ya Rage Ranakun Zuwa Aiki Saboda Tashin Kudin Man Fetur

Gwamna Ya Ƙara Albashi, Ya Rage Ranakun Zuwa Aiki Saboda Tashin Kudin Man Fetur

  • Gwamna Godwin Obaseki ya sanar da cewa sau uku kurum ma’aikata za su rika fita aiki a Edo
  • Cire tallafin fetur ya jawo za a fito da tsarin da za a rika koyar da ‘yan makaranta ta yanar gizo
  • Gwamnatin Obaseki ta kara albashi, babu ma’aikacin da zai tashi da abin da bai kai N40, 000 ba

Edo - A dalilin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya tayi, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ragewa ma’aikata kwanakin zuwa aiki.

Daily Trust ta ce Mai girma Godwin Obaseki ya amince ma’aikatan gwamnatin jiharsa su rika zuwa ofis sau uku a maimakon sau biyar a mako.

A wani jawabi da ya fitar da yamma, Gwamna Obaseki ya ce a matsayinsu na shugabanni a jihohinsu, za su yi kokarin ragewa talaka radadi.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Gwamnan Edo
Gwamna Godwin Obaseki Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC
"Mu na so mu tabbatarwa mutanenmu za mu yi duk abin da za mu iya a bakin ikonmu na gwamnatocin jihohi domin a rage radadin da mutanenmu su ke fuskanta a dalilin halin da ake ciki a yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mun san wahalar da aka shiga a sakamakon tsarin nan, ya jawo karin kudin mota, ya lakume albashin ma’aikatan da ke jihar.
Saboda haka a yanzu gwamnatin jihar Edo ta rage kwanakin zuwa aikin ma’aikatan gwamnati, za su je ofis sau uku a maimakon biyar.

Abin ya shafi malaman makaranta?

Sanarwar ta ce haka zalika gwamnatin Edo ta na tunanin hanyar da za a bi domin rage adadin kwanakin da malaman makaranta za su rika zuwa aiki.

Gwamnan ya ce hukumar SUBEB za tayi karin bayani a kan matakin da za a dauka bayan an kirkiro kafofin koyarwa ta yanar gizo a madadin a shiga aji.

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

Har ila yau, Gwamnatin Obaseki tayi maza ta yanke shawarar a kara mafi karancin albashi.

A maimakon N30, 000 a duk wata, mafi karancin albashin da ma’aikacin gwamnati zai karba a Edo ya koma N40, 000, ana sa ran a nan gaba ya fi haka.

Gwamnatin jihar Kwara

A farkon makon nan, Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya bada wannan umarni a sakamakon tashin da litar fetur ya yi a duk fadin Najeriya.

An samu labari cewa shugabar ma'aikatan jihar Kwara, Misis Susan Modupe Oluwole ce ta sanar da al'umma haka a wani jawabi da ta fitar ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng