Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'addan ISWAP 11 a Jihar Borno

Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'addan ISWAP 11 a Jihar Borno

  • Dakarun sojoji sun samu nasarar tura ƴan ta'addan ISWAP mutum 11 zuwa lahira a wani mummunan farmaki a jihar Borno
  • Dakarun sun samu wannan nasarar ne a wani farmaki da suka kai kan maɓoyar ƴan ta'addan a ƙananan hukumomin Chibok da Damboa
  • Sojojin sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa a hannun ƴan ta'addan bayan sun aika su zuwa inda ba a dawowa

Jihar Borno - Rundunar dakarun sojoji na Operation Hadin Kai (OPHK), tare da haɗin guiwa da Civilian Joint Task Force (CJTF) da Hybrid forces, sun halaka ƴan ta'addan ƙungiyar ta'addanci ta Islamic State of the West African Province (ISWAP), a jihar Borno.

Dakarun sun samu nasarar tura ƴan ta'adda 11 zuwa barzahu a wani mummunan farmaki da suka kai a maɓoyar ƴan ta'addan a dajin Sambisa cikin jihar Borno, rahoton Leadership ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Bayyana Yadda Ya Sha Da Kyar a Hannun 'Yan Daba a Kotu, Ya Nemi Wata Muhimmiyar Alfarma

Dakarun sojoji sun halaka 'yan ta'addan ISWAP 11 a Borno
Sojojin sun kai farmaki ne maboyar 'yan ta'addan Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Ƴa ta'addan sun gamu da ajalinsu ne bayan dakarun sun samu bayanan sirri, inda suka ƙaddamar da farmaki a tsakanin ranakun 31 ga watan Mayu da 4 ga watan Yunin 2023, a maɓoyar ƴan ta'addan a yankin ƙananan hukumomin Chibok da Damboa.

Majiyoyi masu ƙarfi sun sanar da Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa dakarun sojojin sun dira a wasu maɓoyar ƴan ƴan ta'addan a Bale, Tirke, Mandari, Molgoi, Bego, Yarwa, Ngurna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin sun ƙwato makamai masu yawa

Majiyoyin sun tabbatar da cewa a yayin farmakin, an ƙwato makamai da harsasai masu ɗumbin yawa a hannun ƴan ta'addan.

Jihar Borno ta daɗe tana fama da matsalar ta'addanci wacce ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Sai dai, dakarun sojoji a cikin ƴan kwanakin nan na samun galaba sosai akan ƴan ta'addan da suka addabi jihar.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

'Ƴan Ta'addan ISWAP Sun Nutse Cikin Kogi Yayin Tserewa Sojoji

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan ISWAP da dama sun baƙunci lahira bayan sun nutse a cikin ruwa a ƙoƙarin tserewa dakarun sojoji.

Sama da ƴan ta'adda 82 ne da iyalansu suka gamu da ajalinsu bayan sun nutse a cikin ruwan a ƙoƙarin tserewa luguden wuta da dakarun sojoji ke yi musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng