An Shirya Tsaf, Kwatsam 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki da Aka Yi Kus-Kus a Aso Rock

An Shirya Tsaf, Kwatsam 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki da Aka Yi Kus-Kus a Aso Rock

  • Kungiyar NLC ta zauna da gwamnatin tarayya, an lallashi ‘yan kwadago, har sun fasa tafiya yajin-aiki
  • Femi Gbajabiamila ya shaida cewa an cin ma wasu matsaya a sakamakon zaman da suka yi a Aso Rock
  • Shugabannin TUC da NLC sun amince a kafa kwamiti wanda zai yi aiki a kan lamarin karin albashi

Abuja - A karshen zaman da aka yi a yammacin Litinin, kungiyar NLC ta ‘yan kwadago na kasar nan, ta shaida cewa babu maganar shiga yajin-aiki.

The Cable ta ce an cin ma matsaya tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da bangaren ‘yan kwadago, saboda haka sai aka janye shirin da aka yi.

A karshen tattaunawar da aka yi, NLC ta shaida cewa an cin ma yarjejeniya kuma za a fito da wasu matakai da aka dauka bayan janye tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Taimaki APC Wajen Raba Kan ‘Yan Adawa a Zaben Majalisa

Yan Kwadago
Kungiyar 'Yan Kwadago a titi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kungiyar ‘yan kwadagon ta sanar da hakan ne a jawabin bayan taro da shugabannin TUC da NLC da wasu jami’an gwamnati su ka rattabawa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi zaman Litinin

Festus Osifo da Nuhu Toro su ka tsaya a madadin TUC sai Joseph Ajaero da kuma Emmanuel Ugboaja su ka sa hannunsu a madadin kungiyar NLC.

Vanguard ta ce daga bangaren gwamnati akwai Femi Gbajabiamila da sakariyar din-din-din ta ma’aikatar ayyukan yi da kwadago, Kachollom Daju.

Sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya karanto matsayar da aka cin ma bayan zaman, hakan ya tabbatar da ba za a yi wani yajin-aiki ba.

An cin ma matsaya 7 a taron

Kamar yadda shugaban majalisar wakilan mai jiran-gado ya fada, an amince da abubuwa bakwai a cikin yarjejeniyar, daga ciki akwai janye yajin-aiki.

Rt. Hon. Gbajabiamila ya tabbatar da a ranar 19 ga Yuni za a sake yin zama irin haka domin ganin yadda za a aiwatar da alkawuran da aka yi wa ma’aikata.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Mai: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC Ta Fadi Bukatunta

TUC da NLC za su cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya domin a iya shawo kan lamarin.

Gwamnatin tarayya, ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa za su kafa wani kwamitin hadaka wanda zai yi nazari, ya fadi irin karin albashin da ya kamata ayi.

Gwamnatin tarayya, TUC da NLC za su duba tsarin bashin bankin Duniya na rabon kudi tare da neman jefa kananan ma’aikata a cikin wannan tsari.

An yi shirin janye aiki

A baya an samu rahoto cewa malaman asibiti da manema labarai ba za su je wurin aiki daga Larabar nan mai zuwa ba saboda yajin-aikin da NLC ta kira.

Kwamred Leo Isioma Nwenyi ta ce kungiyar SSCUCOEN za ta shiga yajin-aikin na gobe. Hakan na zuwa ne bayan janye tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng