Gwamnatin Tinubu Ta Kara Shiga Sabon Zama da 'Yan Kadugo a Abuja

Gwamnatin Tinubu Ta Kara Shiga Sabon Zama da 'Yan Kadugo a Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta sake komawa ɗakin zaman tattaunawa da wakilan ƙungiyoyin kwadago musamman NLC da TUC
  • Wannan na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya a taron da ya gudana ranar Lahadi tsakanin ɓangarorin guda biyu kan cire tallafin fetur
  • Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya, Femu Gbajabiamila, tsohon shugaban APC na ƙasa da sauransu ke wakiltar FG

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta ci gaba da tattauna wa da wakilan kungiyoyin kwadago a Najeriya yau Litinin 5 ga watan Yuni, 2023 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

FGN na zaman tatttaunawa da wakilan ƙungiyoyin waɗanda suka ƙunshi ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) da kungiyar 'yan kasuwa (TUC) kan matakin cire tallafin man fetur.

FG Da NLC.
Gwamnatin Tinubu Ta Kara Shiga Sabon Zama da 'Yan Kadugo a Abuja Hoto: thecable
Asali: UGC

Taron wanda ya tashi ba tare da fahimtar juna ba ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu, 2023, ana tsammanin cimma matsaya a zaman yau Litinin.

Kara karanta wannan

An Samu Cikas, Kotu Ya Hana NLC da Wasu Ƙungiyoyi Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Mai

Dada Olusegun ne ya tabbatar da ci gaba da ganawar a wani gajeren bidiyon minti ɗaya da daƙiƙu 58 da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A gajeren bidiyon, an hangi wakilan ƙungiyoyin kwadugon sun nemi wuri sun zauna yayin da suke dakon shigowar wakilan gwamnatin tarayya.

Daga cikin waɗanda ke wakiltar gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, a wurin taron sun haɗa da shugaban ma'aikatar fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila, tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, da sauransu.

Kalli Bidiyon ci gaba da zama tsakanin FG da NLC

Daga baya an hangi karisowar wakilan FG karkashin Femi Gbajabiamila kuma daga nan kai tsaye suka ci gaban tattauna wa kan yadda za'a shawo kan lamarin.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tun bayan kalaman shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a wurin rantsuwar kama aiki, "tallafin mai ya tafi" Najeriya ta ɗauki zafi daga kowace shiyya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ma'aikatan Shari'a Na Kasa Sun Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

Tun daga nan dai farashin litar mai ta yi tashin gwauron zabo, daga baya kamfanin mai na kasa (NNPC) ya tabbatar da tashin farashin zuwa sama da N500 kan kowace lita.

Abba Gida-Gida Ya Waiwayi Barayin Kayan Rusau, An Kama Mutum 49

A wani labarin kuma Jami'an yan sanda sun yi ram da wasu da ake zaton yan daba ne masu satar kayan shaguna da sunan ganima a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun samu wannan nasara ne yayin da sabon gwamnan Kano , Abbba Kabir Yusuf, ke ci gaba da aikin rusau a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262