Kwanaki 7 da Mika Mulki, An Fara Maganar Binciken Gwamnatin Muhammadu Buhari
- SERAP ta bada shawarar ayi bincike kan tallafin man fetur da Dalolin da ake zargin sun bace
- Kungiyar mai zaman kanta ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi bincike na musamman
- A lokacin da ake zargin 2.1bn da N3.1tr da sun yi kafa, Muhammadu Buhari yake mulkin Najeriya
Abuja - Kungiyar SERAP ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya binciki kwangilolin tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta bada.
Punch ta rahoto cewa SERAP ta na so Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi bincike a kan tallafin man da ake ikirarin an bada daga 2016 zuwa 2019.
A daidai wadannan shekaru da ake magana, shugaba Muhammadu Buhari ne a karagar mulki.
Wannan kira ya fito ne a wani jawabi da ya fito daga ofishin Mataimakin Darektan SERAP, Kolawole Oluwadare a karshen makon da ya wuce.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Darektan SERAP
Mista Kolawole Oluwadare ya nemi shugaban kasa ya kafa kwamiti na musamman domin gano gaskiyar $2.1bn da N3.1tr da ake zargin sun bace.
"SERAP ta na kira a kafa kwamitin bincike ya yi gaggawar yin bincike a kan zargin $2.1bn da N3.1t da suka bace daga asusun mai da kasafin da aka yi domin biyan kudin tallafin man fetur kamar yadda Akanta Janar ya fada tsakanin 2016 da 2019."
-
A tona asirin marasa gaskiya
Kungiyar ta kuma fadawa shugaban kasa ya fallasa wadanda ake zargi da hannu wajen aikata wannan rashin gaskiya da dukiyar al’ummar kasar.
Baya ga haka, ICIR ta ce SERAP na so a gurfanar da duk wanda ake tuhuma a gaban kotu domin a iya karbo dukiyar al’umma da ta shige aljihunsu.
Lamarin bai tsaya a nan ba, wannan kungiya mai zaman kan ta, ta na so ayi bincike na gaskiya a kan tsarin tallafin fetur tun daga 1999 zuwa yanzu.
Bayan binciken, kungiyar sai ta bada shawarar ayi amfani da kudin da aka gano wajen kawo tsare-tsare da za su rage radadin janye tallafin fetur.
A wasikar da ya rubuta a ranar Asabar, Oluwadare ya ce ba za a taba cigaba idan ana tafka sata ba, ya kuma ce dole ne bi doka wajen cire tsarin tallafin.
A shirya bincike a Kano
An ji labari kungiyar ‘Yan takaran ‘yan jam’iyyar PRP a Kano zaben 2023, ta na rokon a binciki abubuwan da suka faru a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje.
Wadannan ‘yan siyasa sun taya Mai girma Abba Kabir Yusuf murnar rantsar da shi, sun ba shi shawarar ya cigaba da duk wasu ayyukan alheri a jihar Kano.
Asali: Legit.ng