Kamfani Ya Maka Gwamnatin Abba a Kotu, Yana Neman N10bn Saboda Ruguza Otel
- Rushe-rushen da sabuwar Gwamnatin jihar Kano ta ke yi zai jawo ta shiga kotu da wasu manyan ‘yan kasuwa
- Kamfanin Lamash Property Ltd ya shigar da kara, ya bukaci a biya sa N10bn domin an jawo masa asara
- Wasu ‘yan kasuwan sun bayyana yadda aka ruguza masu dukiya a Kano bayan sun kashe Biliyoyin kudi
Kano - Wani kamfani mai suna Lamash Property Limited, ya shaida cewa ya na neman N10bn a matsayin diyyar ruguza masa otel da Daula da aka yi.
Leadership ta ce hakan ya nuna zuwa ne bayan da Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabiru Yusuf ya bada umarni an rusa ginin wannan katafaren otel.
Kamfanin Lamash Property Limited yake cewa a shekarar 2020, Gwamnatin Ganduje ta gayyaci kamfanoni domin a nemi kwangilar sake gina otel din.
Fili ya na hannun gwamnati
A jawabin da aka fitar a ranar Lahadi, shugabannin kamfanin sun ce tun farko ba su taba ikirarin sun mallaki filin wajen ba, ya na hannun gwamnati.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamfanin ya yi mamakin yadda Gwamnan da aka rantsar zai jawo asarar da za tayi sanadiyyar rashin aikin yi kuma a ragewa gwamnati kudin shiga.
Lamash Property Limited ya ce abin da sabuwar gwamnati a karkashin jagorancin NNPP ta ke yi zai jawo ‘yan kasuwa su guji zuba hannun jari a Kano.
Kamar yadda Punch ta kawo rahoto, wannan kamfani ya yi bayanin yadda ya bi ka’ida wajen samun kwangilar har aka kaddamar da aikin a Mayu.
Hajj Camp da wasu gine-gine
Haka zalika kamfanin White Nig. Ltd ya yi tir da matakin da sabon Gwamna ya dauka bayan an shiga yarjejeniyar PPP domin gina sansanin alhazai.
Shugaban kamfanin, Hassan Yusuf Baba ya ce abin takaicin shi ne sai dai su ka tashi da safe, su ka ji labarin ruguza masu gininsu a shafukan sada zumunta.
Shi ma ‘Dan Asabe Abubakar wanda aka ruguza masa shagunan da ya gina a filin sukuwa, ya ce sai da suka kashe abin da ya haura Naira biliyan 1.4.
Alhaji ‘Dan Asabe Aya zargi Gwamnatin Kano da sabawa doka wajen jawowa al’umma asara.
Binciken Dr. Abdullahi Umar Ganduje
A yau ne aka ji labari kungiyar ‘Yan takaran jam'iyyar PRP ta na rokon a binciki abubuwan da suka faru a lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.
Wadannan ‘yan siyasa sun taya Mai girma Abba Kabir Yusuf murnar rantsar da shi, sun ba shi shawarar ya cigaba da duk wasu ayyukan alheri a Kano
Asali: Legit.ng