Tsohon SSG Na Borno, Usman Shuwa, Ya Rasu Kwanaki Bayan Barin Ofis

Tsohon SSG Na Borno, Usman Shuwa, Ya Rasu Kwanaki Bayan Barin Ofis

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Borno, Alhaji Usman Shuwa ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya
  • Shuwa, kafin rasuwarshi ya ajiye aikinsa bisa umarnin Gwamna Zulum kafin rantsar da shi a karo na biyu
  • Marigayin ya rasu a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri (UMTH) da yammacin yau Asabar 3 ga watan Yuni

Jihar Borno - Tsohon Sakataren Gwamnatin Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa ya rasu a yau din nan da yamma.

Shuwa shi ne Sakataren Gwamnatin Borno a gwamnatin Gwamna Zulum kafin rantsar da shi a karo na biyu.

Tsohon SSG Na Borno, Shuwa, ya riga mu gidan gaskiya
Tsohon SSG Na Borno, Usman Shuwa, Ya Rasu Kwanaki Bayan Barin Ofis. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Usman Shuwa, Kafin rasuwarshi shi ne Sakataren Gwamnatin Gwamna Zulum da ya ajiye aiki a ranar 28 ga watan Mayu bisa umarnin gwamnan kafin rantsar da shi a karo na biyu.

Marigayin ya rasu bayan fama da jinya a UMTH, Maiduguri

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Marigayin ya rasu a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri (UMTH) da yammacin yau Asabar 3 ga watan Yuni, cewar jaridar Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shuwa ya kasance gogaggen ma’aikaci wanda ya ke da kwarewa ta musamman a wurare da dama, ya yi aiki da gwamnatin jiha da kuma ta tarayya.

Idan ba a manta ba, yayin ganawa ta karshe da Gwamna Zulum kwanaki kadan kafin ranar rantsarwa, gwamnan ya kara wa marigayin kwanaki uku a ofishinsa bayan wargaza dukkan mukaman da ya nada.

Yaushe aka haifi marigayin, kuma shekarunsa nawa?

Rahotanni sun tabbatar da cewa an haifi marigayin a shekarar 1958, ya rasu ya na da shekaru 65 a duniya bayan fama da jinya.

Gwamna Zulum ya nada Alhaji Usman Shuwa a matsayin Sakataren Gwamnatin Borno a shekarar 2019.

Kafin wannan mukami, ya kasance Sakataren Gwamnatin Borno daga shekarar 2015 zuwa 2019.

Kara karanta wannan

Babban Abokin Faɗan Tinubu Ya Ajiye Kayan Yaƙi, Ya Shirya Zai Karɓi Tayin Kujera

Nan ba da jimawa ake sa ran gwamnatin jihar Borno za ta sanar da lokacin da za a yi sallar jana’izarsa.

An Yi Babban Rashi A Kannywood, Jarumi Kawu Mala Na Shirin 'Dadin Kowa' Ya Rasu

A wani labarin, Aminu Mahmud wanda aka fi sani da Kawu Mala wanda ya kasance shahararren dan kwasan kwaikwayo na Hausa wato Kannywood, ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya shahara ne a shirin nan mai dogon zango na 'Dadin Kowa' wanda ake nuna wa a gidan talabijin na Arewa24.

Asali: Legit.ng

Online view pixel