Ruwan Dare: Yaddajanye Farashin Man Fetur a Najeriya Ya Jawo Tsadar Mai a Jamhuriyar Benin
- Ta bayyana cewa, gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta fara ne da sanar da janye tallafin man fetur ba tare da shirin ‘yan Najeriya ba
- Ya zuwa yanzu, karin farashin man fetur da aka yi a Najeriya ya shafi kasar makwabta ta Benin
- Akwai rahotanni da ke shigo mana cewa, ana kai kayayyakin da suka shafi man fetur zuwa kasar ta Benin a biye ana siyarwa a bakin titi
A bikin rantsar dashi, shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu.
Sanarwar tasa ta jawo nan take dillalan man fetur a kasar suka gallazawa ‘yan kasa ta hanyar garkame gidajen mai, wasu kuma nan take suka kara farashi.
Sai dai, tasirin janye tallafin ba a Najeriya kadai ya tsaya ba, domin kuwa ya tsallaka har kasar Benin da ke makwabtaka da Najeriya.
Yadda tsadar mai a Najeriya ya shafi Benin
Ya zuwa yanzu, farashin man fetur ya karu a Benin, cikin mako guda da ya karu a Najeriya baya janye tallafin na man fetur a nan gida Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar rahoton BBC Pidgin, farashin mai a Benin ya karu jim kadan bayan da Najeriya ta shiga halin ni ‘yasu da aka janye tallafi.
Farashin man fetur a Benin ya karu daga CFA 450 zuwa CFA 700 har na zuwa CF 800 a wuraren, kamar yadda wani mazaunin kasar, Clement Sodji ya bayyana.
Akwai kuma rahotanni da ke cewa, wasu nau’ikan albarkatun mai da ake samarwa a Najeriya kuma suke dauke da tallafi, ana shigar dasu Benin a boye tare da siyar dasu a ain titi.
An kuma tattaro cewa, albarkatun mai na Najeriya na da tasiri ainun ga kasuwanni a kasashen Yammacin Afrika.
Atiku ya caccaki Tinubu kan janye tallafin man fetur
Yayin da Bola Ahmad Tinubu ya kama mulki tare da janyewa ‘yan Najeriya tallafin man fetur, abokin hamayyarsa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya magantu kan lamarin.
A cewar Atiku, bai kamata shugaban na Najeriya ya cire tallafi haka kawai baktatan ba tare da la’akari da wasu bangarori daban-daban ba.
Ya kuma tuna masa yadda gwamnatinsu ta PDP ta yi aikin janye tallafin mai a shekarun mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Asali: Legit.ng