Ba Haka Ake Ba: Atiku Ya Caccaki Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Kamata Ya Yi Kan Tallafin Man Fetur
- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Ahmad Bola Tinubu
- Ya ce bai kamata a janye tallafin man fetur ba tare da ba ‘yan kasa tallafin rage radadi ba, musamman masu karamin karfi
- Tinubu ya janye tallafi, kungiyoyin Najeriya sun bayyana fara yajin aiki da zanga-zanga don maida gwmanati kan turba
FCT, Abuja - Yayin da ake ci gaba da koka yadda gwamnatin Bola Tinubu ta janye tallafin man fetur, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya soki aniyar gwamnatin ta APC.
A bikin rantsar dashi, Tinubu ya bayyana cewa, daga ranar da ya fara jan ragamar Najeriya, to ‘yan kasar sun yi bankwana da tallafin mai, Channels Tv ta ruwaito.
A tun farko, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara bayyana aniyarsa ta janye tallafin a 2022 amma bai cimma hakan ba, wanda Tinubu kuwa ya gaggauta aiwatarwa.
Sai dai, shi kansa Atiku da sauran ‘yan takarar shugaban kasa na 2023, sun bayyana aniyar janye tallafin, amma ta hanyoyi mabambanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya soki gwamnatin Tinubu
A jawabinsa a wajen wani taro a ranar Asabar a jihar Bauchi, Atiku ya soki gwamnatin APC bisa daukar matakin janye tallafin baktatan ba tare da tunani mai zurfi ba, rahoton Vanguard.
A cewarsa:
“A tsakanin 1999 zuwa 2007, gwamnatin PDP ta yi yunkurin cire tallafin man fetur kuma nine na jagoranci kwamitin. Mun cimma cire tallafin man fetur ta hanyoyi guda biyu amma bayan ba da tallafin rage radadi ga wadanda cire tallafin fetur ya shafa.
“Muna da kwarewar hakan a matsayinmu na jam’iyyar da ta yi gwamnati. Abin da ya kamata a yi kenan ba wai kawai sanar da cire tallafin ba ba tare da tattaunawa da wadanda abin ya shafa ba a fannin tattalin arziki.”
Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aikin Gama Gari, Ta Ba Gwamnatin Tinubu Sabon Wa’adi
Kungiyar ‘yan jarida za ta fara yajin aiki da zanga-zanga
A wani labarin, kungiyar ‘yan jarida a Najeriya (NUJ) ta bayyana aniyar fara zanga-zanga da yajin aiki a ranar Laraba 3 ga watan Yuni.
Wannan ya biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi baktatan ba tare da zaman shawari da masu ruwa da tsaki ba.
Kungiyar ta ce tana goyon bayan kungiyar kwadago ta NLC wajen maida gwamnati kan turba a batun zare tallafin na fetur.
Asali: Legit.ng