Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

  • Kungiyar kwadago ta yanke shawarar tafiya yajin-aiki bayan an gagara cin ma matsaya da gwamnati
  • Shugabannin NLC ba su yarda da matakin da sabon shugaban kasa ya dauka a kan tallafin man fetur ba
  • Daga ranar Laraba mai zuwa, ma’aikatan Najeriya za su shiga yajin-aiki da nufin nuna bore ga hukuma

Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa watau NLC ta ayyana shirin fara yajin-aiki a fadin Najeriya daga ranar Laraba mai zuwa.

Rahoton da aka samu a tashar talabijin na Channels ya nuna an dauki matakin ne a dalilin janye tallafin man fetur da aka yi.

Shugaban NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero ya bada sanarwar haka a karshen wani zaman gaggawa da kungiyarsa ta yi.

Tinubu
Bola Tinubu a ofis Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Shugabannin majalisar koli watau NEC ta kungiyar ‘yan kwadagon tayi zama na musamman a garin Abuja domin a tattauna.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Ba Hafsoshin Tsaro Sabon Salon Yaki da Rashin Tsaro a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A karshen zaman, Ajaero ya shaida cewa idan gwamnatin tarayya ta gaa biya masu bukata, za a barke da zanga-zanga a ko ina.

Tinubu ya soke tallafin mai

Bola Tinubu ya hau mulki a ranar Litinin, gwamnatinsa ba ta wuce kwanaki biyar a ofis ba.

Kungiyar ta NLC ta soki yadda sabon shugaban kasan ya soke tsarin tallafin man fetur ba tare da ya zauna da wakilan ma’aikata ba.

Ko da Tinubu ya samu goyon bayan majalisar tarayya da kamfanin NNPCL, kungiyoyi irinsu NLC da TUC duk ba su tare da shi.

A dalilin haka aka yi dogon zama tsakanin bangaren gwamnatin tarayya da NLC domin shawo kan lamarin, amma abin ya gagara.

Zaman ma'aikata da gwamnati

Rahoton ya ce daga gefen gwamnati, akwai Dele Alake, Mele Kolo Kyari, Godwin Emefiele da kuma Kwamred Adams Oshiomhole.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: NNPC Ya Fadi Sabon Shirin Bola Tinubu Tun da Farashi Ya Kai N550

Wadanda suka wakilci ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa a taron su ne: Joe Ajaero da Festus Osifo.

Ma’aikatan kasar sun bukaci gwamnatin tarayya ta janye wannan mataki da ta dauka ba tare da ta fito da wani tsari a madadin tallafin ba.

Akume ya zama SGF

Rahoto ya zo cewa Sanata George Akume aka zaba ya zama sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya, zai gaji Boss Mustapha a Najeriya.

Idan ana maganar sanin aiki, SGF din ya yi mulkin Jiharsa ta Benuwai, ya yi shekaru 8 a Majalisar dattawa, sannan ya rike Ministan tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng