An Tilasta Min Saka Hannu A Sakamakon Zabe, Shaidan Atiku Ya Fada Wa Kotu

An Tilasta Min Saka Hannu A Sakamakon Zabe, Shaidan Atiku Ya Fada Wa Kotu

  • Shaidan dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Kyaftin Agada ya bayyana yadda aka tilasta masa saka hannu a wasu takardu
  • Ya fada wa kotu cewar an tilasta masa saka hannu a sakamakon zaben da bai inganta ba a babban zaben shugaban kasa da aka gudanar
  • Ya tabbatar da cewa jami'an hukumar zabe da kansu ne suka tilasta shi da masa barazanar hana shi kwafin sakamakon na jam'iyyarsa

FCT, Abuja – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a ranar Alhamis ya kira daya daga cikin shaidunsa don bayyana a gaban kotun korafe-korafen zabe na shugaban kasa.

Mai bada shaidan ya fada wa kotun cewa an tilasta masa saka hannu a sakamakon zaben da aka gudanar.

Zaben Najeriya
Yadda Aka Tilasta Min Saka Hannu A Sakamakon Zabe, Shaidan Atiku Ya Fada Wa Kotu. Hoto: Chatham House.
Asali: Facebook

Vanguard ta tattaro shaidan na cewa jami’an hukumar zaben sun ce ba za su bashi dayan kwafi na sakamakon ba don kaiwa jam’iyyarsa idan bai saka hannu ba.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Jihar Arewa Ta Dakatar da Ciyamomi Da Kansiloli a Kananan Hukumomi 17

Shaidan farko daga bangaren Atiku Abubakar, Kyaftin Joe Agada mai ritaya ya fadawa kotu ya kasance shi ne jami’in tattara sakamako na jam’iyyar PDP a jihar Kogi lokacin babban zaben shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana yadda aka tilasta masa saka hannu

Mai ba da shaidan ya fadawa kotu cewa jami’an hukumar zabe sun tilasta masa saka hannu a sakamakon zaben shugaban kasa, cewar Daily Post.

Ya kara da cewa jami’an hukumar zaben sun yi masa barazanar hana shi kwafin sakamakon zaben da zai kai wurin jam’iyyarsa, ya tabbatar da cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa a jihar Kogi.

Ya fadawa kotu cewa fiye da mazabu 20 da ya kaiwa ziyara, ya fahimci yadda aka yi amfani da na’urar BVAS wurin yin magudi a zaben.

A cewarsa:

“Ya mai shari’a, banda inda na kada kuri’ata a kauyen Ogene-Oforachi a unguwar Ogugu na jihar Kogi, na kasance jami’in tattara sakamakon zabe na jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Tinubu Bai Nada Gbajabiamila a Matsayin Shugaban Ma’aikatan Fada ba - Hadiminsa

“Ina da katin shaidar cewa ni ina daga cikin masu aiki a ranar zaben. Katin wanda hukumar zabe ta bani, ya bani damar yawo wuraren da gudanar da zabe.
“Na samu damar zuwa mazabu a karamar hukumata, duk da ban je dukkan mazabun ba.”

Atiku na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa

Atiku da jam’iyyarsa ta PDP suna kalubalantar bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara.

Kotu Ta Dage Sauraran Karar Obi Saboda Rashin Lafiyar Wasu Daga Cikin Lauyoyinsa

A wani labarin, kotun sauraran korafe-korafen zaben shugaban kasa ta daga zamanta saboda rashin lafiyar lauyoyin Peter Obi.

Lauyan dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi, shi ya nemi wannan alfarma a wurin alkalin kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.