Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cire tallafi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu a yayin bikin rantsar da shi
  • Dillalan man fetur a kasar ba su bata lokaci ba wurin rufe gidajen mansu yayin da wasu suka kara farashin litar mai
  • Kungiyar Kwadago, NLC ta yi wani ganawa ta gaggawa da Gwamnatin Tarayya don shawo kan matsalar man fetur

Sa’o’i 72 kenan da dillalan man fetur suke addabi ‘yan Najeriya da tsadar mai tun bayan sanar da cire tallafi da Shugaba Tinubu ya yi a ranar bikin rantsarwarsa.

A kokarin kawo karshen wannan matsalar, Kungiyar Kwadago (NLC) da ta ‘Yan Kasuwa (TUC) da kuma Gwamnatin Tarayya sun yi ganawar gaggawa a ranar Laraba 31 ga watan Mayu.

NLC/Bola Tinubu
Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro Jerin abubuwan da ya kamata a sani dangane da ganawar ta su:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kasa Ta Rincabe Bayan Hawan Tinubu, Gwamnati da Kungiyar Kwadago An Shiga Caccaka Tsinke

1. An shafe sa’o’i ana ganawar

Gidan Talabijin na Channels ta tattaro cewa, ganawar an fara ta ne tun misalin karfe hudu na yamma wanda aka shafe sa’o’i ana yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Joe Ajaero, shugaban NLC a ranar Laraba da safe ya ce ganawar za a fara ne da misalin karfe biyu na rana.

2. Sunayen wadanda suka wakilci Gwamnatin Tarayya

Daga cikin wadanda suka wakilci Shugaba Tinubu akwai tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban NLC, Adams Oshiomhole da shugaban babban bankin Najeriya (CBN), Godswill Emefiele.

Sauran sun hada da tsohon kwamishinan Tinubu a jihar Lagos, Dele Alake da shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari.

3. Wadanda suka wakilci NLC

Kungiyar NLC ta samu wakilcin shugabanta, Ajaero a yayin ganawar, yayinda shugaban TUC, Festus Osifo ya wakilci kungiyarsa a lokacin taron.

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Tinubu Na Ganawar Sirri Da Oshiomhole, NLC Da TUC

4. NLC ta mika bukatunta ga Tinubu

Kungiyar ta ce ya kamata Gwamnatin Tarayya ta mayar da farashin man fetur kaman yadda ya ke kafin halartar wannan ganawar.

Ajaero ya ce rage farashin shi ne zai basu damar samun hanyoyin magance matsalar da kuma kare muradun al’ummar Najeriya.

Kungiyar ta yi alkawarin sake zama da mambobinta saboda sanin matakin da za su dauka na gaba.

5. Alake ya tabbatar da samun nasara a karshe

A yayin da ya ke ganawa da ‘yan jaridu, Alake ya bayyana cewa za su ci gaba da tattaunawa da kungiyar don kawo karshen matsalar.

Kakakin shugaban kasar ya ce za a samu maslaha a karshe inda ya tabbatar da cewa za su kawo karshen matsalar a yayn tattauanawa da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma Kungiyar.

Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗau Zafi, Ya Ce Zai Soke Lasisin Mallakar Duk Gidan Man da Ya Ɓoye Fetur Ko Ya Kara Farashi

A wani labari, an kama tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice a Burtaniya.

An kama ma'auratan ne bisa zargin safarar yara da kuma siyan wani bangare na jikin wani matashi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.