Labari Mai Zafi: Bankin CBN Ya Karyata Labarin Karya Darajar Naira Zuwa N630/$1

Labari Mai Zafi: Bankin CBN Ya Karyata Labarin Karya Darajar Naira Zuwa N630/$1

  • Akwai alamar cewa Babban bankin Najeriya ya karya farashin Naira bayan an yi canjin gwamnati
  • Bayan Bola Tinubu ya hadu da Godwin Emefiele sai aka ji $1 ta koma kusan N639 a kasuwar I & E
  • Tun da aka rantsar da shi, sabon shugaban kasa ya yi alkawarin zai daidaita kan farashin kudin waje

Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN, ya karya darajar Naira a kan Dala inda aka saida kudin Amurkan a kan N631 a maimakon N461.

Wani rahoto da Daily Trust ta fitar a safiyar Alhamis, ya nuna cewa masu shigo da kaya daga kasashen waje sun saye Dala ne jiya a kan N631.

Wannan canji ya na zuwa ne kwanaki kadan bayan Bola Ahmed Tinubu ya karbi mulki, ya na mai alkawarin hada-kan farashin kudin waje.

Kara karanta wannan

Ba a Ba Ni Mukamin Komai ba Inji Wanda Ake Cewa Ya Zama Kakakin Shugaban Kasa

Gwamnan CBN da Tinubu
Buhari, Tinubu, Emefiele da BUA Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Sabon shugaban kasar ya ce zai yi hakan ne domin motsa tattalin arziki. Washegari bayan ya hau mulki, sai ya gana da Mr. Godwin Emefiele.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zaman Emefiele da Tinubu

Har zuwa yau ba a samu labarin bayanin abin da zaman gwamnan CBN da Tinubu ya kunsa ba. Watakila bai rasa nasaba da batun farashin Dalar.

Kafin yanzu, Gwamnan na CBN ya raba farashin kudin kasashen waje a kasuwar canji, farashin babban banki ya bambanta da na ‘yan kasuwa.

Wasu su na ganin salon da Emefiele ya dauka a CBN zai jawo rashin gaskiya, jami’an banki su rika karkatar da Daloli ga ‘yan canji domin a ci riba.

Binciken jaridar ya nuna farashin Dala ya canza a kafar I & E, amma ‘yan kasuwan sun samu duk kudin da suka nema, an samu bambancin N170.

Kara karanta wannan

Ta Tabbata, Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Cire Tallafin Man Fetur, Sabon Farashi Ya Bayyana

Dala a kasuwar canji

A gefe guda, farashin Dala ya sauka a kasuwar canji a makon nan. Daga N750, $1 ta koma N745 a yammacin jiya a garuruwan Kano da kuma Abuja.

Legit.ng Hausa ta duba shafin CBN, kuma har yanzu bankin ya na ikirarin a kan N461.6 ake saida Dalar Amurka, ana sayen kowace a kan N460.6.

Shugaban CPPE, Dr Muda Yusuf wanda masani ne a harkar nan, ya ce idan aka daidaita farashin kudin kasashen waje, N4tr zai shiga asusun tarayya.

A gefe guda, irinsu Farfesa Uche Uwaleke sun ce za a gamu da matsala domin a N435 aka yi lissafin kowace Dala daya a kundin kasafin kudin 2023.

Karya ne - CBN

A wata sanarwa da bankin CBN ya fitar dazu, ya karyata wannan rahoto na karya darajar Naira. Bankin ya ce a ko a yau a kan N406 ya saida Dala.

Kara karanta wannan

Farashin Fetur Ya Kai N600 Zuwa N1200 a Wurare a Ranar Farkon Tinubu a Ofis

Dr. Isa Abdulmumin wanda shi ne babban jami'in sadarwa na rikon kwarya ya musanya labarin, ya na mai yin kira ga mutane su yi watsi da shi.

Tallafin man fetur ya tafi

Game da cire tallafin fetur, an ji labari Ayo Fayose ya na cewa ya yi imani sabon shugaban kasa watau Bola Tinubu ya dauki matakin da ya dace.

Fayose ya yi kira ga mutanen Najeriya su yi hakuri da gwamnatin nan domin wahalar da aka shiga za ta tafi, ya zargi Gwamnatin baya da barna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel