Tsugune Ba Ta Kare Ba: ASUU Ta Maka Gwamnatin Tarayyar Najeriya a Kotu, Ta Fadi Sabon Korafi

Tsugune Ba Ta Kare Ba: ASUU Ta Maka Gwamnatin Tarayyar Najeriya a Kotu, Ta Fadi Sabon Korafi

  • Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan zargin nuna wariya wurin biyan albashin ma’aikata
  • Lauyan kungiyar, Femi Falana ne ya shigar da karar a kotun masana’antu ta Najeriya da ke zamanta a babban birnin tarayya
  • Kungiyar ta shiga yajin aiki mai tsawo a ranar 14 ga watan Fabrairu har zuwa 14 ga watan Oktoba na shekarar 2022

FCT, Abuja – Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta maka Gwamnatin Tarayya a kotu bisa zargin nuna wariya kan biyan albashi da kuma rashin adalci ga mambobinta.

Kungiyar ta shigar da karar ne a kotun masana’antu ta Najeriya a birnin tarayya Abuja ta hannun lauyanta Femi Falana.

Kungiyar ASUU
Kungiyar ASUU Ta Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu, Ta Fadi Sabon Korafi. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Kotun masana’antun a ranar Talata 30 ga watan Mayu tabbatar da dokar Gwamnatin Tarayya na ‘Ba aiki ba biyan albashi’ a karar da gwamnatin ta shigar akan kungiyar.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu Wasu Kungiyoyi 3 Sun Fito Za Su Yaki Bola Tinubu Kan Cire Tallafin Fetur

ASUU ta shafe watanni ta na yajin aiki

A ranar 14 ga watan Faburairu ne dai ASUU ta shiga yajin aiki akan bukatu da dama da suka hada da rashin kayan aiki da gyara albashin malamai da sauransu, cewar TheCable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da a ranar 14 ga watan Oktoba, aka janye yajin aikin duk da ba a cimma wata matsaya ba, Vanguard ta tattaro.

Tun daga watan Faburairu har zuwa Oktoba, Gwamnatin Tarayya ta ki biyan malaman saboda dokar da ta kafa ta ‘Ba aiki ba biyan albashi’.

Mai Shari'a ya yabi tsarin 'Ba aiki ba biyan albashi'

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Benedict Kanyip ya ce ya halatta gwamnati ta rike albashin ma’aikata idan ba su yi aiki ba ko kuma suka shiga yajin aiki, inda ya tabbatar da cewa dokar ta dace.

Kara karanta wannan

Iyalina Ba Su Bukatar Dukiyar Najeriya Domin Mu Rayu Inji Mai Dakin Bola Tinubu

A sabon karar da kungiyar ASUU ta shigar, ta ce akwai nuna bambanci daga Gwamnatin Tarayya musamman yadda suka biya kungiyar likitoci malamai a jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke jihar Anambra wadanda suke yajin aiki tun watan Faburairu na shekarar 2022.

Sannan kungiyar ta kara da cewa, Gwamnatin Tarayya ta biya albashin kungiyar manyan likitoci (NARD) wadanda suke yajin aiki tun watan Satumba na shekarar 2021.

ASUU: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsarin 'Ba Aiki Ba Biyan Albashi'

A wani labarin, hukumar da'ar ma;aikata ta amince da hukuncin 'Ba aiki ba biyan albashi' wanda gwamnatin tarayya ta kawo.

Gwamnatin Tarayya ce ta shigar da kungiyar ASUU kan yajin aiki da malaman ke shafe watanni suna yi ba tare da aiki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.