Farashin Fetur Ya Kai N600 Zuwa N1200 a Wurare a Ranar Farkon Tinubu a Ofis

Farashin Fetur Ya Kai N600 Zuwa N1200 a Wurare a Ranar Farkon Tinubu a Ofis

  • Mutane sun shiga kunci a dalilin rashi ko mummunan tsadar da man fetur ya yi a garuruwa da-dama
  • A jihar Ebonyi, akwai inda litar man fetur ya kai N1, 200 a maimakon N230 da aka saba saidawa a baya
  • Akwai garuruwan da samun man fetur ya yi wahala, jama’a sun komawa ‘yan bumburutu a gefen titi

Ebonyi - A ranar Talata, masu gidajen mai sun kara farashin fetur inda ta kai wasu su na saida kowace lita a kan N1, 200 a Abakaliki, jihar Ebonyi.

Hakan ya na zuwa ne bayan Bola Ahmed Tinubu ya yi maganar janye tallafin man fetur, Daily Trust ta ce hakan ya jefe mutanen Ebonyi cikin wahala.

Mutane sun koma neman fetur ruwa a jallo a sakamakon jawabin sabon shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ba a Ba Ni Mukamin Komai ba Inji Wanda Ake Cewa Ya Zama Kakakin Shugaban Kasa

Budurwa a gidan man fetur
Ma'aikaciya a gidan man fetur Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abin ya fi kamari a Ebonyi

Wani mazaunin garin Abakaliki, Darlington Okeke ya shaidawa manema labarai cewa lita ta tashi daga N230, ya koma tsakanin N800 zuwa N1200.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda wani Ibrahim Ali ya ke fada, ‘yan bumburutu su na saida kowace lita ne a kan N1, 500 yayin da kungiyar ‘yan gidajen mai su ka daina aiki.

Hakan lamarin yake a garuruwa irinsu Legas, Abuja, Ilorin, Benin, Fatawakal, Makurdi da Kano a ranar Talata bayan Bola Tinubu ya shiga ofis.

Dogon layi sun dawo gidaje

Punch ta ce abin ya munana a sakamakon daina saida mai gaba daya da aka yi a wasu gidajen, a inda ake saida man kuma sai mutum ya wahala.

A garin Kalaba, an tashi da dogayen layi a gidajen mai irinsu NNPC, Dozzy da Fynfield. Lita ta koma N400 da N800 a gidajen mai da wajen bumburutu.

Kara karanta wannan

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

Haka lamarin yake a inda ake da fetur a birnin Abuja da garuruwan Neja da Nasarawa.

Jaridar ta ce layin mai ya dawo gidajen da ke aiki a babban birnin jihar Kwara watau Ilorin. Amma akwai gidajen mai a yankin da farashinsu bai canza ba.

Halin da ake ciki a Katsina

A mafi yawan gidajen man da ke Asaba a Delta, sai mutum ya biya N450 zuwa N550 zai samu litar man fetur, a jihohi irin Katsina kuwa, mai ya yi wahala.

Hakan ya jawo sabon Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda ya yi zama da kungiyar IPMAN, kuma bayan taron ya yi umarni da a bude duka gidajen mai.

An fara a sa'a?

Tun a jiya ne rahoto ya zo cewa farashin fetur ya lula daga N210 zuwa fiye da N350 bayan jawabin da Bola Tinubu ya gabatar bayan an rantsar da shi.

Kudin fetur ya fara lulawa sama tun kafin sabon shugaban kasar ya gano kujerarsa. Gidajen mai da-dama sun yi watsi da farashin da aka sani a doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng