Man Fetur: Amfanin Cire Tallafin Mai Guda Biyar Da Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Sani

Man Fetur: Amfanin Cire Tallafin Mai Guda Biyar Da Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Sani

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa babu sauran batun tallafin man fetur daga watan Yuni, saboda babu lissafinsa a cikin kasafin kuɗin bana.

Ya yi batun ne a yayin bikin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasar Najeriya da ya gudana ranar Litinin a Abuja.

Menene tallafin man fetur?

Tallafin man fetur wani nau'i ne na sa hannun gwamnati don rage farashin man fetur ta hanyar ba da tallafin kudaɗe kai tsaye zuwa ga kamfanonin mai, domin su kuma su sauƙaƙa man fetur ɗin ga masu amfani da shi, wato 'yan Najeriya kenan.

Najeriya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu arziƙin ɗanyen mai a Afirka, kuma ta dogara ne kusan kacokan a kan kuɗaɗen da take samu daga ɓangaren man domin bunƙasa tattalin arzikinta.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Matasa 4 Da Buhari Ya Naɗa Da Ake Tunanin Tinubu Zai Cigaba Da Aiki Da Su

Cire tallafin man fetur zai bunkasa tattalin arzikin kasa
Amfanin cire tallafin man fetur ga 'yan Najeriya. Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Nation ta kawo rahoto cewa, an bayyana a cikin kasafin kuɗi na shekarar 2023 cewa za a ƙara tiriliyon N2.557 a cikin kasafin kuɗin domin tallafin man fetur.

Ga wasu guda biyar daga cikin amfanin cire tallafin mai, kamar yadda masana tattalin arziƙi ke hasashe:

1. Bunƙasa ɓangarori daban-daban na ƙasa

Cire tallafin man fetur, a cewar masana, zai taimaka wajen amfani da sauran albarkatun ƙasa da ake da su wajen bunƙasa sauran sassa daban-daban na tattalin arzikin ƙasa.

2. Rage yawan kuɗin kasafin ƙasa

Gwamnati na kashe kaso mai tsoka na kasafin kuɗinta kan tallafin man fetur, wanda zai fi dacewa a kashe su a ɓangaren ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, da dai sauran muhimman abubuwa.

3. Buɗe matatun man fetur a cikin gida

Cire tallafin man zai kuma taimaka wajen kafa ƙarin matatun mai na cikin gida, hakan zai taimaka wajen samar da ƙarin abubuwan da ake samu a cikin man fetur, tare da rage dogaron da Najeriya ke yi kan man da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Shiga Ofis, Ya Faɗi Gaskiya Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur

4. Bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa

A cewar masana da dama, samar da ƙaruwar matatun mai na cikin gida zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa tattalin arzikin kasar.

Zai taimaka ta hanyoyi da dama da suka haɗa da siyar da albarkatu da za a riƙa samu a cikin ɗanyan man zuwa ƙasashen waje, wanda hakan zai ƙarawa Najeriya kuɗaɗen shiga.

5. Samar da ɗumbin ayyukan yi ga 'yan Najeriya

Eagle Online a wani rahoto, ta kawo bayanan da wani masanin tattalin arziki, Dakta Muda Yusuf ya yi kan yadda cire tallafin man zai amfani ƙasar nan.

Ya ce cire tallafin zai sanya a samu ƙarin masu zuba hannun jari a ɓangarori daban-daban, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya.

Farashin mai ya tashi bayan sanar da cire tallafi

A halin da ake ciki, jim kaɗan da sanarwar da sabon shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu ya fitar na cewa gwamnatinsa ba za ta ci-gaba da biyan kuɗaɗen tallafin man fetur ba, an samu hauhawar farashin man a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Wasu gidajen mai sun ninka akan yadda suke siyar da man a baya gabanin wannan sanarwa da sabon shugaban ƙasar ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng