Kotun Koli Ta Zargi PDP da Amfani da Kafafen Sada Zumunta Wajen Hantarar Alkalanta

Kotun Koli Ta Zargi PDP da Amfani da Kafafen Sada Zumunta Wajen Hantarar Alkalanta

  • An zargi jam’iyyar PDP da hantarar alkalan kotun kolin Najeriya bayan da ta kori karar da jam’iyyar ta shigar kan zababban mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima
  • Daya daga cikin mambobin alkalan babbar kotun biyar, mai shari’a Inyang Okoro ya siffanta hakan da rashin kwarewa
  • Kotun kolin kasa a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu ta kori karar da PDP ta shigar na kalubalantar cancantar Sanata Shettima

FCT, Abuja Kotun kolin Najeriya ta zargi jam’iyyar PDP da yiwa alkalan kotun barazana da hantara ta kafar sada zumunta.

Wannan ya faru ne sakamakon yadda kotun ta kori karar da PDP ta shigar da ke kalubalantar cancantar Sanata Kashim Shettima, mataimakin Tinubu.

Kamar yadda ya zo a ruwayar The Cable, mai shari’a Inyang Okoro na kotun koli ya kori karar, inda yace jam’iyyar bata da hurumin gabatar da irin wannan batu ga kotun.

Kara karanta wannan

Mika Mulki: Shugaba Buhari Ya Bayar Da Babban Umurni Ga Osinbajo, Malami Da Sauran Mukarrabansa

Ana zargin PDP da hantarar alkalai
Alkalai a lokacin zaman kotun kolin Najeriya | Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

A bayaninsa na fitowa ne bayan da alkalan kotun duk suka amince da korar karar bayan duba da wasu dalilai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alkali ya caccaki PDP game da hantarar sauran alkalai a shafukan sada zumunta

Mai shari’a Inyang Okoro ya caccaki jam’iyyar PDP, inda yace ya ga gazawa a tsarin jam’iyyar da kuma jin takaicin yadda cikin rashin kwarewa take hantarar alkalan, Punch ta ruwaito.

A cewarsa:

“Yin amfani da kafafen sada zumunta wajen ta’addantarwa da hantarar alkalan kotun koli da wanda ya daukaka kara ke yi abu ne mai ban takaici kuma rashin da’a.
“Daukaka karan bata cancanta ba kuma an yi watsi da ita. Na yi biyayya ne tanadin doka wajen jagorantar hukuncin."

Za a rantsar da Tinubu, Shettima ya ce Tinubu ba zai maida Najeriya kasar Muslunci ba

A wani labarin, kunji yadda zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana matsayar Tinubu da jam’iyyar APC a mulkinsu.

Kara karanta wannan

Abu 3 Da Kotun Koli Ta Yi La'akari Da Su Wajen Korar Karar Da PDP Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima

A cewarsa, Tinubu ba zai iya sauya Najeriya ta zama kasar Muslunci ba, saboda bai iya sauya addinin matarsa da sauran ahalinsa ba duk da kasancewarsa shugabansu a cikin gida.

Ya bayyana hakan ne a martaninsa ga wadanda ke ganin gamayyar Tinubu da Shettima akwai lauje cikin nadi na yiwuwar maida Najeriya kan tafarkin addinin Islama duk da akwai addinai daban-daban a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel