Sarkin Musulmi Ya Ba Bola Tinubu Muhimmiyar Shawara Ana Dab Da Rantsar Da Shi
- A yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, mai martaba Sarkin Musulmi, ya aike da muhimmiyar shawara
- Mai martaba Alhaji Sa'ad Abubakar III ya shawarci Tinubu da ya kawar da kai daga tunanin lashe zaɓe mai zuwa na shekarar 2027
- Mai martaba ya ce a maimakon hakan ya tattara tunaninsa wajen ganin yadda zai ciyar da ƙasar nan gaba saboda al'ummar da za su zo nan gaba
Abuja - Mai martaba Sarkin musulmi, Alhajo Sa'ad Abubakar III, ya ba zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, muhimmiyar shawara kafin ya ɗare kan kujerar mulkin ƙasar nan.
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa, Sarkin musulmin ya shawarci Bola Tinubu da ya kawar da kansa daga yin tunanin lashe zaɓen 2027, a maimakon hakan ya mayar da hankali wajen ganin yadda zai ciyar da ƙasar nan gaba.
Mai martaban ya yi wannan tsokacin ne a birnin tarayya Abuja, a wajen wani taro ranar Asabar, 27 ga watan Mayun 2023, inda tsohon shugaban ƙasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya gabatar da lakca mai taken "Deepening Democracy for Integration and Development."
Sarkin musulmin ya bayyana cewa ƴan siyasa ba wai kawai tunanin yadda za su samu nasara a zaɓen gaba za su riƙa yi ba, yakamata ya yi suna tunanin yadda za a ciyar da ƙasa gaba domin al'umma masu tasowa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa:
"A matsayin ku na shugabannin siyasa, ba kawai ku na buƙatar yin tunani ba ne akan yadda za ku samu nasara a zaɓen gaba, abinda ya fi muhimmanci shine tunani akan al'umma masu tasowa."
"Na bar ku da wannan tunanin sannan ina roƙon Allah ya ba shugabannin mu shiriya, hikima da haƙurin da za su kai ƙasar mu ta kai ga ci. Sannan mu samu zaman lafiya a ƙasar mu mai albarka ta Najeriya."
"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1
Kenyatta ya shawarci Bola Tinubu
Tun da farko, Uhuru Kenyatta, ya ba Tinubu shawarar da ya yi ƙoƙarin janyo a jiki waɗanda ke jin haushin nasarar da ya samu, domin tafiya da kowa a mulkinsa, rahoton The Nation ya tabbatar.
Ya yi nuni da cewa dole ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya jagoranci ƴan ƙasa tare da haɗa kawunan su, ba tare da la'akari da sun zaɓe shi ko basu zaɓe shi ba.
Muhimman Abubuwan Da Tinubu Zai Fara Bayan An Rantsar Da Shi
A wani labarin na daban kuma, kun ji wasu muhimman abubuwa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai fara aiwatarwa da zarar an rantsar da shi.
Abu na farko da Tinubu zai fara yi shine komawa kacokan da zama a fada shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa.
Asali: Legit.ng