Wuta Ta Kona Gidan da Ganduje Zai Zauna Bayan Ya Bar Fadar Gwamnatin Kano
- Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da gobara a gidan da zai koma rayuwa bayan barin gadon mulki
- Gidan Gwamnan Jihar Kano mai barin gado ya na nan Unguwar Nassarawa GRA, tuni har ya tare a ciki
- Ba a san dalilin gobarar ba, amma an tabbatar da ya yi barna a inda Ganduje ya ke kiwon dabbobi a gida
Kano - Gobara ta taba Gidan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje yake shirin komawa da zama yayin da ya bar kan karagar mulkin jihar Kano.
Kamar yadda rahoto mara dadi ya fito daga Punch, gidan Gwamnan mai barin-gado ya na nan a layin Miyanko a Nassarawa GRA Kano.
A ranar Alhamis ma’aikatan kwana-kwana da ke kashe gobara su ka tabbatarwa manema labarai wuta ta barke a gidan a daren Litinin.
Mai magana da yawun bakin jami’an kwana-kana a jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullah ya ce da suka isa gidan, an shawo kan lamarin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wutar ta fara ci ne daga inda Mai girma Abdullahi Ganduje ya ke kiwon shanu, a dalilin haka dabbobi da-dama su ka kone cikin gobarar.
Bayan haka Abdullahi ya ce an yi asarar kadarorin makudan miliyoyin kudi a gidan.
Zuwa yanzu ba za a iya cewa ga abin da ya jawo gobarar ba, Aminiya ta ce ana walda a gidan domin a kammala gyarawa Gwamnan muhallinsa.
Ban san meya faru ba
Da aka tuntubi Sakataren yada labarai na Mai girma Gwamna, Abba Anwar a jiya, sai ya nuna bai da masaniya a game da musibar da ta auku.
Anwar ya ce bai gari a lokacin da abin ya faru a makon nan. Nan da ‘yan kwanaki Ganduje, zai mika mulkin jihar Kano ga Abba Kabir Yusuf.
Wasu su na cewa ba wannan ne karon farko da wuta ta barke a sabon gidan ba, Ganduje tuni har ya bar fadar mulki, ya tare a gidan na sa.
Makarfi v Nasir El-Rufai
Ana da labari Gwamnati mai barin mulki ta Nasir El-Rufai ta karbe wasu filaye tara da Ahmed Muhammad Makarfi ya mallaka a garin Kaduna.
Ana zargin tsohon Gwamnan da kin gina filayen da aka ba shi, ya bada uzurinsa a wasu wasiku da ya aikawa Gwamna, ya na neman alfarma.
Asali: Legit.ng