Rashin Tsaro: Buhari ya Ware N15bn a 2023 Don Kare Dalibai, Cewar Zainab Ahmed

Rashin Tsaro: Buhari ya Ware N15bn a 2023 Don Kare Dalibai, Cewar Zainab Ahmed

  • Ministar kudi da tsare-tsare ta ce gwamnatin tarayya ta ware N15bn don kare dalibai a makaranti
  • Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin 22 ga watan Mayu a Abuja yayin taron bita ga masu gudanarwa
  • Ta ce dole a bai wa makaranti tsaro daga hare-hare don kare wadanda suke makaranta a fadin kasar

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ta ware N15bn a kasafin kudin shekarar 2023 don ba da tsaro ga dalibai da ke makaranta daga hare-hare da kuma masu garkuwa da mutane.

Minstar kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a ranar Litinin 22 ga watan Mayu a Abuja.

Ministan Kudi, Zainab Ahmed
Ministan Kudi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed. Hoto: Tribune
Asali: Facebook

Ta ce don ba da tsaro a makaranti dole a dauki tsauraran matakai don kare na ciki ganin yadda kusan yara miliyan 20 ba sa zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

Zainab Ahmed wadda Hajiya Halima ta wakilce ta, ta kara da cewa ma’aikatar ta ware N15bn musamman don wannan lamari, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta:

“Mun rubutawa ma’aikatun da suke da hakkin sakin wadannan kudade da su ba mu don aiwatar da wannan abin da muka sa a gaba.
“Muna da tsari tun shekarar 2022 da ma’aikatarmu ta tsara tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi don kare yara ‘yan makaranta. Muna son mu yi musu bita yadda za su yi amfani da shi a wuraren da suke daban-daban."

Bayani daga bakin kwamandan hukumar NSCDC

Kwamandan hukumar NSCDC, Dakta Ahmed Abubakar Audi yayin kaddamar da bitar ya ce kashi 75% na yaran daga sansanin ‘yan gudun hijira suke da ba su da wata hanyar da za su koyi wani abu, cewar Punch.

A cewarsa:

“Iyaye da dama suna tsoron kai ‘ya’yansu makaranta wadda hakan ya kara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar."

Kara karanta wannan

Kotu ta Hana a Taba ‘Dan Majalisar Kano, Ado Doguwa Bisa Zargin Kashe Mutane

An dauki wannan mataki ne ganin yadda jami’an NSCDC ke kare dukiyoyin gwamnati wadda ya hada da makaranti da duk wani abu da ya shafi ma’aikatun ilimi.

Ba Zai Yiwu a Kwashe Daliban Najeriya Daga Sudan Ba – Gwamnatin Tarayya

A wani labarin, gwamanatin tarayya ta ce ba zai yiwu ba a kankanin lokaci a kwaso 'yan Najeriya dalibai da ke makale a kasar Sudan.

Dalibai da dama 'yan Najeriya ne ke makale a kasar tun bayan fara rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.