Yanzu Yanzu: Ba Zai Yiwu a Kwashe Daliban Najeriya Daga Sudan Ba – Gwamnatin Tarayya

Yanzu Yanzu: Ba Zai Yiwu a Kwashe Daliban Najeriya Daga Sudan Ba – Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana yin duk mai yiwuwa don ganin ta kare yan kasarta da ke Sudan
  • FG ta ce an tanadi komai don kwaso dabilai da yan kasar da ke tsare a kasar da ake yaki amma hakan na da hatsari kuma ba mai yiwuwa bane a yanzu
  • Shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta ce an kona jirage da ke filin jirgin saman kasar

Gwamnatin tarayya ta ce kwaso yan Najeriya da ke kasar Sudan ba abu ne mai yiwuwa ba a yanzu haka, Daily Trust ta rahoto.

Yan Najeriya da yakin Sudan da ke gudana ya ritsa da su suna ta roko da a zo a kwashe su.

Fiye da mutum 300 ne aka kashe tun bayan da yakin ya fara a ranar Asabar tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaban hafsan sojojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Daglo, wanda shine kwamandan mayakan RSF.

Kara karanta wannan

An Ga Tashin Hankali Yan Bindiga Sun Budewa Yan Sanda 5 Wuta Yayin Da Suke Tsakar Cin Abinci A Ranar Idi A Imo

Abike Dabiri-Erewa
Yanzu Yanzu: Ba Zai Yiwu a Kwashe Daliban Najeriya Daga Sudan Ba – Gwamnatin Tarayya Hoto: Businessday NG
Asali: UGC

Hukumomin gwamnati na kokarin kwaso yan Najeriya a Sudan amma ba mai yiwuwa bane, Dabiri-Erewa

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, shugabar hukumar da ke kula da yan Najeriya mazauna waje, Abike Dabiri-Erewa ta ce hukumar Najeriya a Sudan da hukumar NEMA sun tanadi komai don kwashe daliban Najeriya da sauran yan kasar da ke tsare a Sudan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai ta ce halin da ake ciki a yanzu sun sa hakan na da matukar hatsari kuma ba zai yiwu kowani jirgi ya tashi ba a wannan lokaci.

Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Gabriel Odu na sashin labaran hukumar NIDCOM, ta nakalto Dabiri-Erewa na cewa jiragen da aka ajiye a filin jirgin saman kasar sun kone a safiyar Juma'a.

Ta ce kungiyoyin agaji na neman hanyoyin kaiwa mutane abinci, ruwa da magungun, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

“Na Matsu Na Koma Mahaifata Daura”: Inji Buhari Yayin da Ya Yi Bikin Sallah Na Karshe a Aso-Rock

Wani bangare na sanarwar ya ce:

"Shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna waje, Hon Abike Dabiri-Erewa ta ce yayin da hukumar Najeriya a Sudan da hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA), suka yi tanadi don kwashe daliban Najeriya da sauran yan kasar da ke tsare a Sudan, tashin hankalin da ake ciki ya sa hakan na da hatsari kuma ba zai yiwu kowani jirgi ya tashi ba a wannan lokaci, tana mai cewa an kona jiragen da aka ajiye a filin jirgin saman kasar a safiyar jiya."

Bikin mika mulki: Na kagu na koma Daura, Buhari

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya matsu ya mika mulki a ranar 29 ga watan Afrilu domin ya tattara ya koma mahaifarsa a garin Daura, jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel