Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sa Hannu, Ya Kawo Dokoki 8 a Makon Karshensa a Ofis
- Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a wasu daga cikin kudirorin da ‘yan majalisa suka amince da su
- Kudirorin sun shiga cikin dokokin kasa a lokacin da ‘yan kwadanki kadan suka rage a canza gwamnati
- Dokokin za su bada damar taimakawa marasa karfi, samar da ayyukan yi da inganta karatu a Najeriya
Abuja - A daidai lokacin da yake shirye-shiryen barin ofis, sai aka ji Mai girma Muhammadu Buhari ya amince da wasu kudirori da suka zama dokoki.
A ranar Litinin, Mai taimakawa shugaban kasa wajen harkokin majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare ya ce kudirori takwas sun shiga dokokin kasa.
The Nation ta ce Babajide Omoworare ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar a garin Abuja.
Hadimin shugaban na Najeriya ya ce Muhammadu Buhari ya amince da kudirorin da suka fito daga majalisa kamar yadda tsarin mulkin kasa ya ba shi iko.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kudirorin majalisar tarayya da suka samu karbuwa a wajen Mai girma shugaban kasa mai barin-gado akwai kudirin tsarin inganta rayuwar marasa galihu.
An samu jami'o'i da cibiyoyi
Baya ga kudirin kafa hukumar NSIP akwai kudirin ilmin karatun sakandare da kudirin da ya bada damar kafa jami’ar kiwon lafiya a garin Azare a Bauchi.
Haka zalika doka ta tabbatar da kafa wata jami’ar kiwon lafiya da ke Ila-Orangun a jihar Osun.
Kamar yadda rahoton da aka fitar a jiya ya nuna, sababbin dokokin da aka fito da su za su inganta ilmin kwarewa a harkar akantanci da sanin kan aikin ofis.
Omoworare ya ce kudirin kula da aikin Injiniyoyin wuta zai tabbatar akwai majalisar da ke kula da wannan fanni da kokarin tantance kwararrun Injiniyoyi.
Da yake magana a shafin Twitter, mai taimakawa shugaban kasa a kafofin sadarwa na zamani watau Bashir Ahmaad, ya jero wadannan sababbin dokoki.
Kudirorin da suka zama dokoki
1. National Social Investment Programme Agency
2. National Senior Secondary Education
3. Federal University of Health Sciences Ila-Orangun (Establishment)
4. Federal University of Health Sciences, Azare (Establishment)
5. Chartered Institute of Development Studies and Administration of Nigeria (Establishment)
6. Federal Institute of Industrial Research (Establishment)
7. Institute of Strategic Management of Nigeria
Ayi bincikien nadin mukamai
A makon jiya kurum, an ji labari Philip Agbese ya na korafi saboda Shugaban kasa ya raba mukamai fiye da 10 alhali wa’adinsa ya na neman zuwa karshe.
Jagoran na APC ya ce yabbatar da Toyin Madein a kujerar Akanta Janar da aka yi ya nuna ba za a rasa rashin gaskiyar da ake shukawa a gwamnati ba.
Asali: Legit.ng