Tinubu, Dangote Da Abdulsamad Sun Kashe Kuɗi Sama Da N500m Don Sayen Littafin Shugaba Buhari
- Manyan 'yan kasuwa da manyan 'yan siyasa ne suka halarci taron ƙaddamar da wasu littattafai guda biyu da aka rubuta kan mulkin Buhari
- Abdulsamad Rabiu, Aliko Dangote da Tinubu na cikin mahalarta taron da kuma suka sayi litattafan da kuɗaɗe masu yawa
- An rubuta litattafan ne kan abubuwan da suka wakana a zamanin mulkin shugaba Muhammadu Buhari
Abuja - A yau Juma'a ne dai aka ƙaddamar da wasu litattafai guda biyu da aka rubuta kan abubuwan da suka shafi mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Mahalarta taron bikin ƙaddamar da litattafan guda biyu sun kashe kuɗaɗe sama da naira miliyan ɗari biyar (N500m) domin samun kwafinsu, kamar yadda jaridar Punch ta yi rahoto.
Sanata Abu Ibrahim da Goldman suka rubuta litattafan
Shugaban ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo ne ya jagoranci ƙaddamar da littattafan a bikin da aka gudanar a babban ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Littattafan da aka ƙaddamar su ne: “State of Repair: How Muhammadu Buhari Tried to Change Nigeria for Good” wanda Antony Goldman ya rubuta.
Sannan sai kuma ɗayan mai taken: “The Legacy of Muhammadu Buhari” wanda tsohon sanatan Katsina ta kudu, Abu Ibrahim ya rubuta.
Abdulsamad BUA ya sayi kwafi akan N200m
Attajirin nan shugaban rukunin kamfanoni na BUA, Abdulsamad Isiyaka Rabiu ne ya jagoranci siyan kwafin littattafan akan kuɗi N200m.
Bayan nan kuma sai shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da kuma shugaban kamfanin Oriental Energy Resources, Muhammed Idimi suka sayi kwafin littattafan biyu akan N100m kowanne.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, suma ba a barsu a baya ba. Su biyun sun haɗu inda suka sayi duka kwafi biyun akan kuɗi naira miliyan 40.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi da mataimakin shugaban jami’ar Abuja, Farfesa Abubakar Abba ne suka duba littattafan gabanin wallafa shi.
A jiya Alhamis ne jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa shugaban ƙasar Ghana, Akufo-Addo ne zai zo domin ƙaddamar da litattafan na Muhammadu Buhari.
Babu buƙatar wani shugaba ya sake fita waje neman lafiya
A wani labarin da muka wallafa a baya, uwargidan shugaban ƙasa mai barin gado Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana cewa, daga yanzu babu buƙatar wani shugaban ƙasa ya ƙara fita waje neman lafiya.
Ta bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da katafaren asibitin gidan gwamnati na N21b da shugaba Buhari ya ƙaddamar a Abuja.
Asali: Legit.ng