Musulmi Da Musulmi: Kwamitin Koli Na Shari'a Ya Kare El-Rufa'i, Ya Ragargaji CAN

Musulmi Da Musulmi: Kwamitin Koli Na Shari'a Ya Kare El-Rufa'i, Ya Ragargaji CAN

  • Kwamitin Koli na Shari'a ta Najeriya ta yi martani ga CAN kan kalaman El-Rufai inda ta goyi bayan tsohon gwamnan na Kaduna
  • El-Rufai a kwanakin baya ya bayyana cewa a siyasance babu dalilin da za bawa kirista takarar mataimakin gwamna tunda suna iya cin zabeko ba kiristoci
  • Kwamitin Koli ta ce a jihar da musulmi suka kai kaso 75 cikin 100 babu dalilin ba wa kirista takarar mataimakin gwamna

Kwamitin Koli na Shari'a a Najeriya, a ranar Lahadi, tayi martani don goyon bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan wani faifan bidiyo mai mintuna shida da ya bazu shafukan sada zumunta, wanda ya bayyana dalilinsa na ba wa musulmai mukamai a gwamnatinsa.

Kwamitin Kolin Na Shari'a Ta Kare El-Rufai
Kwamitin Koli Na Shari'a Ya Kare El-Rufa'i Kan Kalamansa Game Da Tikitin Musulmi Da Musulmi. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

A cikin bidiyon an jiyo El-Rufai yana fada wa wasu malaman addinin musulunci ranar da zai bar kujerar gwamna, cewa:

Kara karanta wannan

Rusau a Kano: APC Ta Maida Raddi Ga Gwamna Abba Gida-Gida, Ta Roke Shi Alfarma 1

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Me yasa na zabi Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ta zama mataimakiyata a 2019? Da farko, nayi lissafi na gano cewa yawancin wanda ba musulmi ba basa zabar jam'iyyarmu (APC). Yawanci. Toh, meyasa zan ba su kujerar mataimaki?
"Nayi lissafi na kuma sani zamu iya cin zabe ba tare da basu takarar mataimaki ba. Shine dalili na farko. Siyasa ce, kana so ka ci zabe, kana neman wanda za su zabe ka. Mun kula cewa tun da muka fara dimukradiyya, mun san inda muke cin zabe da inda muke faduwa. Mun yi lissafi a siyasance. Wannan shi ne dalili a siyasance."

Amma shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, a wata tattaunawa da Arise TV, ya soki El-Rufai game da kalaman.

Sai dai, kungiyar sharia, a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi ta hannun sakatarenta, AbdurRahman Hassan, ta kare El-Rufai, tare da bayyana kalaman CAN a matsayin munafinci, Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Garabasa: 'Yan Twitter sun more, Elon Musk zai fara raba musu kudi, amma da sharadi

Kungiyar ta ce:

"Tsawon sati guda, kungiyar CAN, reshen Jihar Kaduna na ta kumfar baki, suna zargin Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai, ta yin wasu kalaman tunzuri a wajen CAN, saboda kawai ya bayyana ra'ayinsa game da takarar Muslim-Muslim.
"Lokacin kamfen din zabukan da suka gabata a kasar nan, ina kungiyar CAN ta shiga lokacin da mafi yawan malaman coci ke kalamai marasa kan gado, wanda ba don kiyayewar Allah ba, da Najeriya ta zama tarihi.
"Ina CAN ta shiga lokacin da wani fasto ya fito da AK-47 kan mumbari a Abuja? Ina CAN ta shiga lokacin da wasu malamansu suka dinga hasashen banza ga kasar nan? Amma Alhamdulillah, duk hayaniyar da surutan karyar, babu wani mummunan abu da ya faru da kasarmu, Najeriya.
"Al'ummar musulmi sun yi juriya, in ba don haka, ta yaya a jihar da ke da mafi rinjayen musulmi kamar Taraba kirista zai zama gwamna. Idan a Jihar Plateau da ke da sama da kaso 35 na musulmi ba a basu takarar mataimakin gwamna, me yasa a Jihar Kaduna, da ke da kusan kaso 75 na musulmi, ace ba za ayi takarar Muslim-Muslim ba?

Kara karanta wannan

Kafa tarihi: Emefiele ya kafa tarihi, a zamaninsa ne darajar Naira ta fi karyewa a idon duniya

"Malaman kirki kullum wa'azin zaman lafiya su ke yi, ba rikici ko tada hargitsi ba, wanda daga baya zai iya zama barazana ga zaman lafiya da cigaba. Muna kira ga CAN da ta fita daga sha'anin siyasa, maimakon tsoma baki a kan komai."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164