Za Su Sace Ni: Wani Fitaccen Dan Siyasar Najeriya Ya Bar Kasa, Ya Yi Zargin Ana Barazana Ga Rayuwarsa
- Dan takarar gwamnan PDP ya bayyana yadda ya shiga tashin hankali bayan kammala zaben gwamnan bana a jihar Ogun
- A cewarsa, yanzu haka ya buya a wata kasa saboda yadda ake barazana da rayuwarsa, kamar yadda yace ya samu bayanai
- An bayyana yadda ya sha kaye da kuma yadda ya tunkari kotu game da sakamakon zaben gwamnan bana da aka yi a jihar
Dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a zaben ranar 18 ga watan Maris a jihar Ogun, Ladi Adebutu, ya ce ya gudu ya buya bayan wata barazana ga rayuwarsa da ake yi, Premium Times ta ruwaito.
Mista Adebutu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Saturday Tribune, inda ya ce yana magana ne daga wani boyayyen wuri a wajen Najeriya; bai bayyana ainihin inda yake ba.
Ya ce ya yanke shawarar buya ne bayan da hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ta janye jami’anta da ke ttsare shi, haka nan an rage yawan ‘yan sandan da ke tare dashi.
Yadda ya sha kaye a zaben gwamnan jihar
Idan baku manta ba, Mista Adebutu ya samu kuri’u 262,383 a zaben da Gwamna Dapo Abiodun na jam’iyyar APC ya lashe da kuri’u 276,298.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika, ya shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamna domin kalubalantar ayyana Abiodun a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ya yi zargin cewa, an yi aringizon kuri’un da suka wuce gona da iri da kuma karya dukkan dokokin kudin zabe na Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa, adadin kuri’un da aka soke ya zarce tazarar da Mista Abiodun yake bashi a zaben da aka kammala.
A cewarsa, tun lokacin da ya kai kara gaban kotun, yake fama da lallashi da kuma barazanar ya janye karar kwata-kwata.
Na kadu bayan da SSS suka janye jami’ansu
Ya ce ya ji mummunan tashin hankali bayan da hukumar SSS ta janye jami’anta ga kuma ‘yan sanda sun rage nasu jami’an daga gareshi.
Ya kara da cewa, yana da sahihan bayanan sirri da ke nuna ana kokarin sace shi kafin yanke hukunci kan karar da ya shigar.
A cewarsa cikin hirar:
"Allah ba zai bar mugun shirinsu ya tabbata ba. Shi ya sa na yanke shawarar ci gaba da gudun hijirar kaina don kare kaina."
Ba wannan ne karon farko, a watan Afrilu ya bayyana irin wannan batu na bibiyarsa da ake za a hallaka shi, rahoton Daily Post.
PDP ta fara azumi don nasarar Atiku a kotu
A wani labarin, 'yan jam'iyyar PDP za su yi azumi domin tabbatar da nasarar Atiku Abubakar a gaban kotu.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake kokarin shari'a kan karar da ya shigar na kalubalantar sakamakon zaben bana.
Asali: Legit.ng