Goro a Miya: Wasu Shugabannin APC Sun Kebe da Makiyin Tinubu, Tsohon Shugaba a PDP
- Jiga-jigan jam’iyyar APC sun shiga wata ganawar sirri da jigon PDP, Olubode George game da yadda Tinubu zai yi mulkin kasar nan
- Ana kyautata zaton za su shawo an George ne kan ya daina sukar Bola Ahmad Tinubu a kafafen yada labarai
- Ya zuwa yanzu, ba a san a hukumance dalilin wannan ganawar ba, amma an bayyana wadanda suka shiga ganawar da shugaban na PDP
Jihar Legas - Wasu shugabannin jam’iyyar APC yanzu haka suna cikin wata ganawa da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Olabode George, rahoton Vanguard.
Shugabannin an APC da ke ganawar sun hada da shugaban majalisar shawarwari kan shugabanci ta GAC, uwar jam’iyyar a Legas, Prince Tajudden Olusi babban mai ba Buhari shawari kan SDGs da kuma tsohuwar mataimakiyar gwamnan Legas, Mrs Adejoke Orelope-Adefulire.
Rahoto bayyana dalilin wannan zama ba, amma dai ana kyautata zaton shugabannin na APC suna duba hanyar nemawa Tinubu gata da mutunci ne a idon George gabanin fara mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu.
Meye dalilin wannan ganawar?
An kuma tattaro cewa, shugabannin na APC suna nema da kuma rokon Bode George da ya tsakaita wuta da sukar Tinubu a kafafen yada labarai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan baku manta ba, George ya kasance daya daga cikin masu sukar Tinubu kuma yake bayyana rashin amincewarsa da fitowar sabon shugaban a zaben bana.
Tun bayan da Bola Ahmad Tinubu ya zabi abokin takara Musulmi mutane da yawa daga yankunan kasar nan ke bayyana rashin amincewa da adawarsu da zabin dan takarar na shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki.
Kamata ya yi matar Tinubu ta zuba masa guba, inji wani fasto
A wani labarin, wani fasto ya gamu da fushin ‘yan Najeriya a kafar sada zumunta yayin da ya bayyana bakar kiyayyarsa ga Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a Najeriya.
Faston ya tofa kalamai maras dadi a wani bidiyon da aka yada, inda yace da tuni Tinubu da yanzu ba a kai ga Peter Obi ya rasa mulkin kasar nan ba kamar yadda ya faru a zaben 2023.
‘Yan Najeriya sun bayyana bacin rai da fushi, inda suka nemi a gaggauta kame faston tare da yi masa titsiye don neman bahasi.
Asali: Legit.ng