Shugaba Buhari Zai Sauka Daga Kan Mulki, Nnamdi Kanu Yana Garkame a Kurkuku

Shugaba Buhari Zai Sauka Daga Kan Mulki, Nnamdi Kanu Yana Garkame a Kurkuku

  • A zaman da aka yi na karshe a ranar Alhamis Kotun koli ta sa lokacin sauraron karar Nnamdi Kanu
  • Sai ranar 14 ga watan Satumba sannan Alkalan Kotun koli za ta kula karar shugaban kungiyar IPOB
  • Tun a 2021 Kanu yake shari’a da gwamnatin tarayya, Muhammadu Buhari zai bar mulki yana garkame

Abuja - Kotun koli ta daga sauraron karar da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar a gabanta sai zuwa watan Satumba mai zuwa.

Tashar talabijin Channels ta rahoto cewa sai ranar 14 ga watan Satumban 2023 sannan Alkalan kotun koli za su saurari karar Nnamdi Kanu.

Mazi Kanu ya daukaka kara a babban kotun kasar, ya na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ta hana hukumar DSS ta fito da shi.

Nnamdi Kanu
Magoya bayan IPOB da Nnamdi Kanu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A zaman karshe da aka yi a ranar Alhamis, kotun kolin Najeriya ta amince da rokon da Ministan shari’a watau Abubakar Malami ya gabatar.

Kara karanta wannan

Mata Ta Sumar Da Mijinta Bayan Ta Lakada Masa Duka a Jihar Lagos

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban lauyan gwamnatin tarayya ya bukaci ya kara shigar da wasu kara domin maida martani ga Kanu wanda ya shafe shekaru biyu a tsare.

Lokaci ya kurewa Alkalai

Kotun Allah ya isar ta ce idan ta amince ta saurari martanin gwamnati, ba ta da wani lokaci da za ta iya zartar da hukunci nan da kwanaki 90.

Ganin ba za a iya cin ma wa’adin ba, tashar ta ce aka daga karar zuwa tsakiyar Satumba.

Abin da wannan mataki da aka dauka ya ke nufi shi ne sai kusan watanni hudu bayan Muhammadu Buhari ya bar ofis sannan za a cigaba da shari’ar.

Kanu da kungiyarsa ta IPOB sun rika sukar gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta, har ta kai ana zarginsu da laifin cin amanar kasa.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Roki Majalisa Ta Bada Damar Ya Karbo Aron $800m a Karshen Mulkinsa

Premium Times ta ce kafin yanzu, Mai shari’a Haruna Tsammani da wasu Alkalai sun amince da rokon da Lauyoyin gwamnatin su ka gabatar.

Shari'ar Kanu da Hukuma

A Yunin 2021 aka dawo da Kanu Najeriya da karfi da yaki daga kasar Kenya, zuwa Afrilu aka ji labari cewa kotu ta soke wasu zargin da ake yi masa

Da aka yi zaman kotu a Oktoban 2022, Alkali ya wanke shugaban na IPOB daga sauran laifuffuka bakwai, kafin a sake shigar da wata sabuwar kara.

Jami'a a garin Kwale

An samu rahoto Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege ya yi nasara, an kai wata sabuwar jami’ar tarayya zuwa jihar Delta.

Ovie Omo-Agege ya yi magana ta bakin Sunny Areh, ya ce mutanen yankin Ndokwa za su amfana da jami’ar kiwon lafiyar da za a gina a garin Kwale.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng