Bai Bani Lokaci Ba: Dan Haya Ya Maka Mai Gida a Kotu Kan Watsar Da Kayansa

Bai Bani Lokaci Ba: Dan Haya Ya Maka Mai Gida a Kotu Kan Watsar Da Kayansa

  • Wani mai haya ya maka mai gidan hayan nasa a kotu bisa zargin wulakanci da watsar masa da kaya
  • Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Benedict ne ya jaddada haka inda ya ce haka ya sabawa doka
  • Mai karan ya na zargin mai gidan da tafka masa gagarumar sata da ta kai akalla kimanin kudi N144,000

Jihar Lagos - Wani mai haya a jihar Lagos ya maka mai gidan da yake haya, Ganiu Tajudden a kotu a ranar Laraba 10 ga watan Mayu bisa zargin watsar masa da kaya da ya yi ba tare da ya ba shi lokaci ba.

Ana zargin mai gidan hayan da laifuka guda 4 da ya hada da rashin bin tsarin doka wurin fitar da dan hayan da kuma kawo tsaiko ga zaman lafiya, jaridar Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Roki Majalisa Ta Bada Damar Ya Karbo Aron $800m a Karshen Mulkinsa

Kotu/Dan haya/Mai Gidan Haya/Legas
Gudumar Kotu. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Benedict Aigbokhan ya fada wa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata mummunan laifin a ranar 27 ga watan Afrilu da misalin karfe 10:30 na safe a hanyar St. Laisu da ke Ikotun ta jihar Lagos.

Ya kara da cewa wanda ake+ karan ya shiga gidan Mista Olamilekan Oloyode ya kwashe kayansa ya watsar bayan kudin hayarsa ta kare, ya ce mai gidan bai bi hanyar da ta dace ba na bashi lokaci wadatacce amma sai ya dauki hukunci da hannunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun tattaro cewa Aigbokhan ya ce mai gidan ya sace wa wanda ke karan kaya da ya kai kimanin N144,000.

Ya ce daga cikin kayan akwai injin bada wuta da ya kai N50,000, sai dutsen guga na N10,000 da talabijin babba da kudinsa ya kai N70,000, sannan kwanon rufi na N14,000.

Kara karanta wannan

Hayan Gidan N2m a Shekara a Legas: Babu Ruwa, Ga Tsadar Wutan Lantarki

Hukuncin mai shari'a

Mai shari’a, Miss K. A. Ariyo ta bada belin wanda ake karan akan kudi N100,000 da kuma wadanda zasu tsaya masa da suke da aikin yi da kuma shaidan biyan kudin haraji ga gwamnatin jihar Lagos.

Miss Ariyo ta dage sauraron karar hai sai ranar 22 ga watan Mayu.

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Basaraken Da Ya Yi Barazanar Kawo IPOB Legas

Wata kotu a yankin Yaba a jihar Legas ta bada belin shugaban kabilar Ibo mazauna Ajawo a jihar, Fredrick Nwajagu wanda ya yi barazanar, kawo 'yan kungiyar IPOB Lagos.

An tusa keyar Fredrick ne zuwa kotu bisa zarginsa da ake na alwashin kawo ‘yan ta’addan IPOB cikin jihar Legas a hirarsa da ya yi gidan talabijin na Channels.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.