‘Yan Bindiga Sun Fito da ‘Yan Matan da Suka Dauke a FGC Yauri Bayan Watanni 23 a Jeji

‘Yan Bindiga Sun Fito da ‘Yan Matan da Suka Dauke a FGC Yauri Bayan Watanni 23 a Jeji

  • Wasu daga cikin daliban makarantar gwamnatin FGC Yauri da aka yi garkuwa da su, sun kubuta
  • Shugaban kungiyar iyayen da aka dauke ‘ya ‘yansu daga makarantar ya tabbatar da haka a jiya
  • Salim Kaoje ya ce mata uku sun samu ‘yanci a karshen tattaunawar da aka yi da ‘yan bindiga

Kebbi - Mata uku daga cikin bakwai na daliban makarantar gwamnatin tarayyar nan da ke Birnin Yauri a jihar Kebbi da suke tsare, sun samu ‘yanci.

A rahoton Daily Trust na ranar Talata aka fahimci cewa miyagun ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da wadannan dalibai tun a 2021, sun fito da su yanzu.

Shugaban kungiyar da iyayen wadannan dalibai suka kafa, Malam Salim Kaoje ya sanar da cewa ‘yan bindigan sun sake sakin dalibai uku a makon jiya.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Babban Sarki, Sun Sace Yayansa Da Jikoki 9 Da Wasu Mutane

'Yan bindiga
Ana fama da rashin tsaro a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Da yake bayani a farkon makon nan, Salim Kaoje ya ce sun yi kwanaki shida su na tattaunawa da ‘yan bindigan a cikin jeji kafin cin ma nasarar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunayen wadanda aka ceto

Daliban da suka samu ‘yanci su ne Elizabeth Ogechi Nwafor, Esther Sunday da Aliya Abubakar.

Tun a ranar Litinin, wadannan ‘yan makaranta suka isa jihar Kebbi kamar yadda Salim Kaoje ya fada, sun shafe kusan shekaru biyu a hannun miyagu.

Da yake bayani a lokacin, mahaifin daya daga cikin daliban na FGC Yauri ya ce Elizabeth, Esther da Aliya su na hannun jami’an gwamnatin jihar Kebbi.

Wannan mutumi bai iya shaidawa jaridar ko sai da aka biya kudin fansa kafin matan su shaki iskar ‘yanci ba, iyakarta dai ya ce sun fito bayan an sasanta.

“Eh, sun fito da uku daga cikin dalibanmu a yammacin Lahadi. Yanzu haka su na hannun gwamnatin jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Fadar Sarki a Kaduna, Sun Sace 'Ya'Yansa da Jikoki

- Salim Kaoje

Shekaru kusan 2 kenan

A watan Yuni za a cika shekaru biyu da dauke dalibai 96 daga makarantar ta Birnin Yauri.

Gutsun-gutsun ake fito da wadannan ‘yan makaranta, a mafi yawan lokuta sai an biya ‘yan bindiga kudi a matsayin fansa kafin iyaye su ga ‘ya ‘yansu.

Ana gina abubuwan more rayuwa

A wani labarin mai faranta rai, an ji Muhammadu Buhari ya gina hanyoyin kilomita 9,290.34, sannan an daura alamu 254,690 a kan titunan tarayya.

Ministan ayyuka da gidaje na Najeriya, Tunde Fashola ya ce a shekaru 4, FEC ta amince a gina ko a gyara tituna 155, sannan ana gina gidaje 6, 000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng