'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Masu Gudanar Da Bauta a Jihar Kaduna
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki wata coci a jiɓar Kaduna, inda suka yo awon gaba ɗa mutane da dama
- Ƴan bindigan sun dira cikin cocin ne a ƙaramar hukumar Chikun ana tsaka da gudanar da harkokin bauta na ranar Lahadi
- Mutum 40 ƴan bindigan suka yi awon gaɓa da su, sai dai wasu mutum 15 daga ciko sun samu sun dawo
Jihar Kaduna - Ƴan ta'addan da suka dira a coci a ƙaramar Chikun ta jihar Kaduna, sun yi awon gaba da masu bauta mutum 40.
Shugaban hukumar kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihar Kaduna, Rev Joseph John Hayab, ya bayyana cewa mutum 15 daga cikin waɗanda aka sacen sun dawo wajen iyalan su, cewar rahoton Vanguard.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Kiristoci (CAN) ta jihar Kaduna, ya rabawa manema labarai a jihar Kaduna, ranar Litinin, ya bayyana cewa:
"Kusan mutum 40 ƴan bindiga suka sace a ranar Lahadi, yayin gudanar ibada a cocin Bege Baptist, Madala akan titin hanyar Buruku Baringi cikin ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An sace mutanen ne ranar Lahadi da misalin ƙarfe 9:30 na safe lokacin da suka ji ƙarar bindiga a kusa da cocin. Ƴan bindigar sun farmaki cocin, sannan suka ayi awon gaba da mutum 40."
"Akan hanyar su, mutum 15 daga cikin waɗanda aka sacen sun dawo, yayin ds. ragowar mutum 25 ɗin na hannun ɓata garin da suka ce, ba tare da sun ce komai ba."
Hayab ya kuma ƙara da cewa ana cigaba da.ƙoƙarin ganin an tuntuɓi miyagun kan ragowar sauran mutum 25 ɗin da suka sace, cewar rahoton Sahara Reporters.
Gwamnatin jihar da rundunar ƴan sandan jihar, ba su ce komai ba dangane da sace mutanen masu gudanar da bauta da aka yi ba.
Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC, Wasu 'Yan Takara Sun Yi Bore
Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Babban Sarki, Sun Sace Yayansa Da Jikoki 9 Da Wasu Mutane
Da zu rahoto ya zo kan yadda ƴan bindiga suka je har fadar babban sarkin Kagarko a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan a yayin farmakin da suka kai fadar, sun yi awon gaba da.wasu daga cikin ƴaƴansa da jikokin sa.
Asali: Legit.ng