Auren Dole: Wata Budurwa Ta Maka Mahaifinta a Gaban Kotu
- Wata matashiyar budurwa ta maka mahaifinta a gaban kotu saboda yana shirin yi mata auren dole
- Budurwar mai suna Fatima ta garzaya wata kotun shari'ar musulunci ne a Kaduna, inda ta kai koken ta
- Ta nemi kotun da ta hana mahaifinta aurar da ita ga wanda ya ke so ta aura a ƙauye, saboda tana da wanda ta ke so
Jihar Kaduna - Wata budurwa mai suna Fatima mai shekara 20 a duniya, ta nemi wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a Kaduna, a ranar Litinin, da ta hana mahaifinta mai suna Aliyu Muhammad, yi mata auren dole.
Punch ta kawo rahoto cewa, mai shigar da ƙarar ta hannun lauyanta, Malam Y.A Bulama, ta gayawa kotun cewa tana da wanda ta ke so.
"Mahaifinta yana son ta auri wani mutum a ƙauyen su da ke jihar Niger. Yanzu haka tana zaune ne a gidan gwaggon ta, saboda ya yi mata barazanar kai ta ƙauyen ya aurar da ita." A cewar lauyan.
"Da Na Kowa Ne": Uwa Ta Fadi Yadda Lakcara Ya Kore Ta a Aji Don Kukan Jinjiranta, Bidiyon Ya Janyo Cece-Kuce
Ya yi nuni da cewa mai shigar da ƙarar ba ta kawo ƙarar mahaifinta ba domin ta ci masa mutunci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A na sa bangaren, mahaifin budurwar, ya bayyana cewa iyayen sa da suka rasu, su ne suka zaɓar mata wanda za ta aura lokacin suna raye, sannan yana son ya ga ya mutunta burin su.
"Na aurar da ƴaƴana mata guda shida a ƙauye kuma suna zaune lafiya. Mahaifiyar Fatima itace ta ke kitsa mata wannan taurin kan."
"Ina buƙatar na yi shawara da mutane na kan wannan lamarin."
Alƙalin kotun, mai shari'a Malam Isiyaku Abdulrahman, ya tabbatar da cewa uba yana da hurumin zaɓar wa ɗiyar sa mijin da zata aura a ƙarƙashin shari'ar musulunci.
Sai dai, ya yi nuni da cewa ba a son yin auren dole, inda ya shawarci wanda ake ƙarar da ya zama mai hakuri da ɗiyar sa, cewar rahoton The Nigeria Lawyer.
"Kai mahaifinta ne, saboda haka addu'a zaka yi kan abinda ya fiye mata alkhairi, saboda idan ka yi fushi da ita, ba za ta ga da kyau ba." A cewar alƙalin
"Ka bari ta kawo wanda ta ke so ta aura, idan kaga ka yadda da addinin sa da halayensa, ka aura mata shi."
Ya kuma shawarci mai shigar da ƙarar da ta kasance ɗiya mai biyayya.
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani malami wanda ya kira kansa da ɗalibin ilmi, mai suna Malam Adam Muhammad. Malamin ya yi bayanin cewa duk da mahaifi yana da ikon zaɓar mijin aure ga ƴar sa, kuskure ne ya aura mata wanda bata so.
Ya yi bayanin cewa, kamata ya yi ya nuna mata nagartar wanda ya ke son ya aura mata ɗin, sannan idan ta kawo wani ya ga bai yarda da nagartar sa ba, ya nuna mata illolin da ke tare da auren sa.
"Soyayyar Nesa Akwai Wuya": Matashi Ya Sharbi Kuka Yayin Da Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya Zata Koma Kasarsu
Malamin ya kuma yi bayanin cewa, idan dai har yarinyar ba ta bi wasu hanyoyi ba, kafin kai mahaifin na ta ƙara kotu, misali gayawa na gaba da shi cewa ba ta son zaɓin da ya yi mata, to akwai kuskure babba, ta kai shi kai tsaye ƙara a kotu.
Tsaffin Hotunan Ekeremadu Tare Da Sarki Charles III Ya Janyo Muhawara A Intanet
A wani labarin na daban kuma, wasu tsaffin hotunan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ikweremadu, sun janyo cece-kuce a intanet.
A cikin hotunan an nuna Ikweremadu tare da sabon sarkin Ingila, Sarki Charles III.
Asali: Legit.ng